By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Sami Tserewar Fursunoni 281 a Maiduguri Sanadiyar Ambaliyar Ruwa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Sami Tserewar Fursunoni 281 a Maiduguri Sanadiyar Ambaliyar Ruwa
News

An Sami Tserewar Fursunoni 281 a Maiduguri Sanadiyar Ambaliyar Ruwa

Attajdid
Last updated: 2024/09/16 at 9:44 AM
Attajdid Published September 16, 2024
Share
SHARE

Fursunoni kusan 300 suka tsere bayan ambaliyar ruwa a Maiduguri sanadiyar wata mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a Maiduguri da ta rusa katangar wani gidan yari a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya a farkon makon da ya gabata, lamarin da ya bai wa fursunoni 281 damar tserewa, in ji hukumomin gidan yarin a ranar Lahadi.

An sake kama bakwai daga cikin fursunonin da suka tsere a wani samame da jami’an tsaro suka gudanar, kamar yadda Umar Abubakar, mai magana da yawun hukumar gidan yari ta Nijeriya ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar.

“Ambaliyar ta rusa katangar gidajen gyara halin da suka hada da Cibiyar Kula da Matsakaicin Tsaro, da ta rukunin gidajen ma’aikatanta da ke cikin birnin,” in ji Abubakar.Ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan nemo da mayar da sauran fursunonin.

Maiduguri babban birnin jihar Borno, ya fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru da dama, a farkon makon da ya gabata.

Ambaliyar ta fara ne a lokacin da wata madatsar ruwa ta cika bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, lamarin da ya lalata gidan namun dajin na jihar tare da kora kadoji da macizai a cikin al’ummomin da ambaliyar ta mamaye.

Ambaliyar ta kashe akalla mutum 30 a cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, sannan ta shafi wasu miliyan guda, tare da tilasta wa dubban mutane komawa sansanonin ‘yan gudun hijira.

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 16, 2024 September 16, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Kasuwar Yankaba Za Ta Fara Tantance Masu Talla Biyo bayan Daura Aure Kan Naira 500 A Kano

Attajdid Attajdid October 19, 2024
Mata Sunyi Muzahara a Yemen
Substantiating Governor Umar Namadi’s Stance Against Call for Self-Défense
Ko ECOWAS za ta iya jure wa ƙalubalen da ke gabanta?
Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?