By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Netanyahu da Gallant Suna Fuskantar Fishin Kotun ICC Kan Yakin Kare-Dangi da Suke Yi a Palestine.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Netanyahu da Gallant Suna Fuskantar Fishin Kotun ICC Kan Yakin Kare-Dangi da Suke Yi a Palestine.
International News

Netanyahu da Gallant Suna Fuskantar Fishin Kotun ICC Kan Yakin Kare-Dangi da Suke Yi a Palestine.

Attajdid
Last updated: 2024/09/01 at 4:06 PM
Attajdid Published September 1, 2024
Share
SHARE

Isra’ila ta matsa wa ICC lamba a kan ta jinkirta sammacin kama Netanyahu da GallantYayin da Isra’ila ta yi Allah wadai tare da yin watsi da bukatar mai gabatar da ƙara, har yanzu babu tabbas kan yadda Isra’ila za ta mayar da martani idan aka bayar da sammacin kama mutanen biyu.Kotun ICC ta bukaci a ba da sammacin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant.

Isra’ila na matsa wa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ta jinkirta bayar da sammacin kame Firaminista Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaƙi a Gaza, a cewar kafar yada labaran Isra’ila.

Majiyoyin hukuma sun ce Isra’ila na matsin lamba na diflomasiyya kan kotun da ke Hague don jinkirta sammacin kama mutanen biyu.”Yana da wuya a iya hasashen yadda wadannan matakan za su yi tasiri ga hukuncin alkalan,” in ji jaridar Haaretz a ranar Laraba.A ranar 20 ga watan Mayu mai shigar da ƙara na kotun ICC, Karim Khan, ya ce ya buƙaci sammacin kama Netanyahu da Gallant kan laifukan cin zarafin bil adama da laifukan yaƙi a Gaza.

Yayin da Isra’ila ta yi Allah wadai tare da yin watsi da buƙatar mai gabatar da ƙara, har yanzu babu tabbas kan yadda Isra’ila za ta mayar da martani idan aka bayar da sammacin kama shi.

A cewar Haaretz, jami’an Isra’ila a yanzu sun shagaltu da tantance ko kotun ta ICC na da hurumin yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi rikicin Falasdinu da Isra’ila.Yanzu haka dai kwamitin alkalan kotun ICC na nazarin bukatar sammacin da Khan ya gabatar, wanda zai bukaci yanke hukunci kan lamarin.

Rashin amincewa da kotunKafin yanke hukunci, alkalan za su sake duba ra’ayoyin shari’a da kasashe da dama da kungiyoyin kasa da kasa suka gabatar game da sammacin da aka nema.

“Duk da haka, jami’an Isra’ila ba su san tsawon lokacin da wannan aikin bitar zai dauka ba,” in ji Haaretz.

Isra’ila ba mamba ce a kotun ta ICC, yayin da Falasdinu ta amince da zama mamba a 2015.Kotun ta ICC, wadda aka kafa a shekara ta 2002, kungiya ce ta kasa da kasa mai zaman kanta wadda ba ta da alaka da Majalisar Dinkin Duniya ko wata cibiya ta kasa da kasa, kuma hukunce-hukuncenta na da nasaba.

Duk da yadda Isra’ila ta yi watsi da hurumin kotun ta ICC, kotun ta shafi yankunan Falasdinawa da ta mamaye tun shekara ta 1967, inda ta ba ta damar gurfanar da jami’an Isra’ila da ake zargi da aikata laifuka a wadannan yankuna.

A wata hira da CNN a ranar 21 ga Mayu, mai gabatar da ƙara na ICC Khan ya bayyana cewa an yi masa barazana yayin da yake binciken jami’an Isra’ila.

Jami’an Isra’ila na yanzu da na baya sun yi watsi da matakin Khan, saboda rashin amincewa da hurumin kotun.

Sun zargi kotun ta ICC da ƙyamar Yahudawa tare da yin kira ga ƙawayen Isra’ila da su janye kudade tare da rusa kotun. TRT AFRIKA HAUSA

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 1, 2024 September 1, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Gwamnatin Jihar Sokoto ta ƙaddamar da wani sabon shiri na tilasta wa duk ma’aikatan lafiya da gwamnati ta ɗauki nauyin karatunsu yin aikin shekara biyu a yankunan karkara bayan kammala karatu.

Attajdid Attajdid August 6, 2025
Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis
Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji
Yahudawa Sun yi Zanga-zangar Kyamar Kisan Kare-dangi ga Palesdinawa
GOV. LAWAL FLAGS OFF CONSTRUCTION OF 200-BED CAPACITY AT TALATA MAFARA GENERAL HOSPITAL, PROCURES ADVANCED MEDICAL EQUIPMENT.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?