By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Kotu a Nijeriya ta samu ‘yan China 4 da laifin hakar ma’adanai ba da lasisi ba
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Kotu a Nijeriya ta samu ‘yan China 4 da laifin hakar ma’adanai ba da lasisi ba
News

Kotu a Nijeriya ta samu ‘yan China 4 da laifin hakar ma’adanai ba da lasisi ba

Attajdid
Last updated: 2025/05/16 at 9:17 AM
Attajdid Published May 16, 2025
Share
SHARE

Kotu a Nijeriya ta samu ‘yan China 4 da laifin hakar ma’adanai ba da lasisi ba

Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arziƙi Ta’annati a Nijeriya, EFCC, ta yi nasara a ƙarar da ta kai wasu ‘yan China huɗu da ta kama da laifin ayyukan haƙar ma’adanai a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

EFCC ce ta kama mutanen ta gurfanar da su / EFCC

13 awanni baya

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi ta’annati a Nijeriya, EFCC, ta ce ta samu nasarar hukunta wasu ‘yan China da laifin haƙar ma’adanai a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

 

An yanke wa waɗanda ake zargin su huɗu, Liang Quin Yong, da Wang Huajie, da Zhong Jiajing, da Long Kechong, hukuncin zaman gidan-kaso na shekaru biyar-biyar saboda laifin.

 

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis 15 ga Mayu, ta ce tun a watan Maris ne aka kama su a wani filin haƙar ma’adanai na kamfanin haƙar ma’adanai mai suna “JLM Mining” a jihar Plateau.

 

Hukumar ta ce kame ya zo ne bayan samun bayanan sirri kan ‘yan Chinan da ake zargi da haramtattun ayyuka a Jos, babbar birnin jihar Plateau.

 

Sanarwar ta tabbatar da cewa alƙaliyar babbar kotun tarayya da ke Jos babban birnin jihar Plateau, Mai Shari’a Dorcas V. Agishi ta samu ‘yan China huɗu da laifin da ya jiɓinci haramtattun ayyukan neman ma’adanai.

 

Bayan kotun ta karanta wa mutanen laifukan da ake zarginsu, sun amsa laifin, inda lauyoyin EFCC, M.O. Arumemi da F.A.I Asemebo suka roƙi kotu ta hukunta su daidai da laifinsu.

 

A ƙarshe, alƙaliyar ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, sannan ta yankewa ‘yan Chinan huɗu hukuncin shekaru biyar kowannensu, da kuma tarar miliyan guda kowannensu.

 

Haka nan, kotun ta ba da umarnin korar baƙin daga Nijeriya da kuma haramta musu sake shigowa ƙasar. Sannan za a ƙwace dukiyoyin da suka mallaka a bai wa gwamnatin tarayya.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 16, 2025 May 16, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.

Attajdid Attajdid May 16, 2025
The Bauchi State governor, Bala Mohammed, has disclosed that he and others in his government are ready to sacrifice their lives for the people to live
ABIBATI TINUBU MEMORIAL QUR’ANIC RECITATION COMPETITION: A CELEBRATION OF MOTHERHOOD, FAITH, AND LEGACY
Tinubu na Son Majalisar Dokokin Nijeriya ta Amince ya Karbo Bashin N1.77
Jigawa Speaker empowers 2,018 Constituents 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?