Jam’iyyar NNPP wadda Dakta Boniface Aniebonam ya kafa a shekarar 2001, ta samu ƙarfi sosai a Jihar Kano bayan tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga cikinta a shekarar 2022 tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.
Shigowarsa ta farfaɗo da jam’iyyar, inda ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2023 ta hanyar lashe kujerar gwamna da wasu kujerun majalisa.
Sai dai rikicin cikin gida da na shugabanci sun dabaibaye jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa ficewar wasu manyan ’ya’yanta zuwa APC, lamarin da ke haifar da tambaya kan makomar NNPP a Kano.
Mai rahoto
Mustapha Garba Usman




