By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sudan ta shigar da ƙorafi ga AU cewa Chadi na samar wa ‘yan tawaye makamai
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Sudan ta shigar da ƙorafi ga AU cewa Chadi na samar wa ‘yan tawaye makamai
International News

Sudan ta shigar da ƙorafi ga AU cewa Chadi na samar wa ‘yan tawaye makamai

Attajdid
Last updated: 2024/11/05 at 9:38 PM
Attajdid Published November 5, 2024
Share
SHARE

Sojojin Sudan da ke samun goyon bayan gwamnatin ƙasar sun zargi maƙwabciyarta Chadi da samar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye, mai yiwuwa tana nufin dakarun sa-kai da take fafatawa da su.

 

Ministan Shari’a Muawiya Osman ya ce a ranar Talata gwamnatin Burhan ta kai karar kasar Chadi gaban kungiyar Tarayyar Afirka.

 

Da yake magana da manema labarai, ciki har da AFP, Osman ya ce gwamnati ta buƙaci a biya ta diyya, ya kuma zargi Chadi da “sayar da makamai ga mayakan ‘yan tawaye” da kuma “illata ‘yan kasar Sudan”.

 

“Za mu gabatar da shaidu ga hukumomin da abin ya shafa,” in ji shi daga Port Sudan, inda Burhan ya koma bayan fada ya bazu zuwa babban birnin kasar, Khartoum.

 

An raba fiye da mutum miliyan 11 da muhallansu

 

A watan jiya ne kasar Chadi ta musanta zargin da ake mata na cewa tana “kara habaka yakin Sudan” ta hanyar bai wa kungiyar RSF makamai.

 

“Ba ma goyon bayan wani bangare da ke yaki a kasar Sudan – muna goyon bayan zaman lafiya,” in ji ministan harkokin wajen kasar kuma kakakin gwamnati Abderaman Koulamallah a lokacin.

 

Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da mashigar Adre da ke tsakanin kasashen biyu wajen kai kayan agaji.

 

Tun da farko Sudan ta amince ta ci gaba da bude mashigar na tsawon watanni uku, wanda zai kare a ranar 15 ga watan Nuwamba.

 

Hukumomin birnin Khartoum dai ba su yanke shawarar tsawaita shirin ba.

 

Yakin basasar Sudan ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane tare da raba fiye da miliyan 11 da muhallansu, ciki har da miliyan 3.1 da a yanzu ke mafaka a kan iyakokin kasar.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 5, 2024 November 5, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu’a

Attajdid Attajdid November 4, 2024
Substantiating Governor Umar Namadi’s Stance Against Call for Self-Défense
Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4
IGP Deploys DIG To Oversee Security For Ondo Governorship   
Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?