By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul
News

Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul

Attajdid
Last updated: 2025/05/25 at 3:16 PM
Attajdid Published May 25, 2025
Share
SHARE

Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul

 

Erdogan ya karɓi baƙuncin al Sharaa a ranar Asabar inda aka gudanar da bikin tarbarsa a hukumance a Ofishin Shugaban Ƙasa na Dolmabahce da ke Istanbul.

 

 

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gana da shugaban ƙasar Syria, Ahmad al Sharaa, a birnin Istanbul.

 

Erdogan ya karɓi baƙuncin al Sharaa a ranar Asabar inda aka gudanar da bikin tarbarsa a hukumance a Ofishin Shugaban Ƙasa na Dolmabahce da ke Istanbul.

 

Taron ya samu halartar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Tsaron Ƙasa Yasar Guler, Shugaban Leƙen Asirin Turkiyya Ibrahim Kalin, Shugaban Ma’aikatar Masana’antar Tsaro ta Turkiyya Haluk Gorgun, Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al Shaibani da wasu jami’ai da dama.

 

An gudanar da taron ne ƙofa a garƙame.

 

Tattaunawar ta zo ne bayan da Amurka da Tarayyar Turai suka fara ɗage takunkumin da suka ƙaƙaba wa Syria, kuma ziyarar da al Sharaa ya kai Turkiyya ita ce ta farko tun bayan ɗaukar matakin.

 

Shugaba Erdogan ya yi maraba da matakin, yana mai cewa, Turkiyya na kallon sassauta takunkumin ta fuska mai kyau. Ya jaddada muhimmancin kiyaye iyakokin kasar ta Syria da tabbatar da mulkin ƙasar a ƙarƙashin hukuma guda ɗaya.

 

Erdogan ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa Syria na tafiya a kan hanya mai kyau kuma tana kan hanyar samun zaman lafiya, inda ya kuma ƙara jaddada goyon bayan da Turkiyya ta jima tana bayarwa.

 

“Kamar yadda muke tare da Syria har zuwa yanzu, za mu ci gaba da yin haka,” kamar yadda ya bayyana a lokacin tattaunawar.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

AT-TAJDID NEWS

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 25, 2025 May 25, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News

Syrian Rebel Commander Addresses Crowds After Victory

Attajdid Attajdid December 10, 2024
Jigawa Offers 30% Input Subsidy to Rice Farmers
Shuwagabannin Hamas na Siyasa Sun Canja Salo a Kasashan Kitare
Manajan bankin Keystone reshen Gusau ya Musulunta a yau
Wasu Kerin Hare-haren Asa Musa da Netsani Oz
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?