By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Dakatar da Bai wa Afirka ta Kudu Tallafi Saboda ta Kai Isra’ila ƙara Kotun Duniya Kan Yaƙin Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > An Dakatar da Bai wa Afirka ta Kudu Tallafi Saboda ta Kai Isra’ila ƙara Kotun Duniya Kan Yaƙin Gaza
International News

An Dakatar da Bai wa Afirka ta Kudu Tallafi Saboda ta Kai Isra’ila ƙara Kotun Duniya Kan Yaƙin Gaza

Attajdid
Last updated: 2025/02/10 at 8:34 AM
Attajdid Published February 10, 2025
Share
SHARE

Shugaban Amurka Donald Trump ya saka hannu kan wata doka wadda za ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi, inda Fadar White House ta bayyana dalilan hakan da batun ƙarar da Afirka ta Kudun ta shigar gaban Kotun Duniya kan Isra’ila da kuma rashin amincewarta game da sabon tsarin filaye.

 

“Muddin Afirka ta Kudu za ta ci gaba da tallafa wa miyagu a fagen siyasar duniya tare da ba da damar kai hare-hare a kan tsirarun manoma da ba su ji ba ba su gani ba, Amurka za ta daina ba da taimakon da take bai wa kasar,” in ji Fadar White House.

 

Washington ta koka kan shari’ar da Afirka ta Kudu ta gabatar a gaban kotun ICJ, inda ta zargi Isra’ila da kisan kiyashi kan kisan gillar da Tel Aviv ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban Falasdinawa tare da haddasa rikicin bil adama.

 

Amurka ta bayar da wannan a matsayin wani misali na yadda Afirka ta Kudu ke nuna ta ja daga tsakanin Washington da ƙawayenta.

 

Haka kuma Trump ya yi Allah wadai da tsaron filaye na Afirka ta Kudu.

 

Fadar White House a ranar Juma’a ta ce Washington za ta gudanar da wani shiri na musamman na tsugunar da manoman Afirka ta Kudu da iyalansu a matsayin ‘yan gudun hijira.

 

Ta ce jami’an Amurka za su dauki matakan ba da fifiko wajen bayar da agajin jin kai, da suka hada da karbar baki da kuma sake tsugunar da su ta hanyar shirin shigar da ‘yan gudun hijira na Amurka ga ‘yan ƙabilar Afrikaners a Afirka ta Kudu, wadanda galibinsu fararen fata da asalinsu mazauna Holland da Faransa.

TRT African Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid February 10, 2025 February 10, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Anti-Corruption Commission Decries Legal Delay , Recorded 479 Cases , in 2025

Attajdid Attajdid December 10, 2025
Yan Wasan Kano Pillars Sun Yi Hadari
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
Jigawa Speaker Calls for Global Action on Girls’ Education, Security, and Safety
ConflictMyanmar regime labels key ethnic armed groups ‘terrorist’ organisations.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?