Netanyahu Yana Tsoran Za a Kawo Masa Hari Daga Lebanon
An ɓoye Firaministan Isra’ila Netanyahu a wani wuri mai tsaro a asibiti bayan an ji ƙarar jiniya.
An garzaya da Firaminista Benjamin Netanyahu wani wuri mai cikakken tsaro a cikin asibiti da ke arewacin Isra’ila bayan an ji ƙarar jiniya da ke nuna yiwuwar kai masa harin roka daga Lebanon ranar Lahadi.
Lokacin da jiniyar ta yi ƙara, Netanyahu yana Asibitin Hillel Yaffe da ke birnin Hadera, inda ya ziyarci sojojin Isra’ila da suka jikkata sakamakon harin jirgi mara matuƙi da ƙungiyar Hezbollah ta kai musu inda ta kashe huɗu daga cikinsu tare da jikkata gommai, a cewar kafar watsa labaran gwamnatin Isra’ila KAN.
Bayan jin ƙarar jiniyar, jami’an tsaron da ke tare da Netanyahu sun ɗauke shi zuwa wani wuri mai cikakken tsaro da ke cikin asibitin, in ji KAN.
Yaƙin da mahukuntan Isra’ila, Yahudawan sahyoniyya sun kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,289. A gefe guda, hare-haren da Isra’ila ta ƙadamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,309 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.
At-tajdid News.




