By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Yarjejeniyar Gaza na Cikin Hadari Yayin da Sojojin Isra’ila Suka Cigaba da Kai Hari
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Yarjejeniyar Gaza na Cikin Hadari Yayin da Sojojin Isra’ila Suka Cigaba da Kai Hari
International News

Yarjejeniyar Gaza na Cikin Hadari Yayin da Sojojin Isra’ila Suka Cigaba da Kai Hari

Attajdid
Last updated: 2025/01/17 at 6:46 AM
Attajdid Published January 17, 2025
Share
SHARE

Yarjejeniyar Gaza na Cikin Hadari Yayin da Sojojin Isra’ila Suka Cigaba da Kai Hari Kuma Netanyahu ya Jinkirta Taron Majalisar Ministocin Isra’ila

 

 

Duk da sanarwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza, lamarin da ya janyo asarar rayukan fararen hula.

 

Wasu shaidun sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa wani jirgi mara matuki na Isra’ila ya kai hari kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yammacin birnin Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, lamarin da ya haddasa jikkata mutane da dama ciki har da yara.

 

Hukumomin lafiya har yanzu ba su ce komai ba kan lamarin ko kuma bayyana adadin wadanda suka jikkata.

 

Shaidu sun kara da cewa, jami’an kare farar hula da sauran jama’a sun garzaya wurin da lamarin ya faru domin kashe gobarar da ta tashi a cikin tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu.

 

Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce majalisar ministocinsa ba za ta yi taro don amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ba, yana mai zargin kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas da haifar da “rikici a ƙurarren lokaci”.

 

Ba tare da yin karin haske ba, ofishin Netanyahu ya zargi Hamas da yin watsi da wasu sassan yarjejeniyar a wani yunƙuri na “karɓar rangwame a minti na ƙarshe”.

 

Majalisar zartarwar Isra’ila ta shirya amincewa da yarjejeniyar ranar Alhamis.

 

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya yi maraba da labarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu yayin da take ci gaba da mara baya ga samar da kasashe biyu.

 

Lula ya yaba da labarin a shafinsa na X yayin da ya bayyana bukatar bangarorin biyu su tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

 

“Bayan tsananin wahala da barna, labarin cewa a karshe an cimma matsaya kan tsagaita bude wuta a Gaza ya kawo kyakkyawar fata, da fatan kawo karshen rikicin da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su, su taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa da za ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.” “in ji shi.

TRT African Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid January 17, 2025 January 17, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Kungiyar Human Rights Watch ta Kalubalanci Isra’ila da Amurka 

Attajdid Attajdid August 1, 2025
Mohamed Salah ya zama gwarzon ɗan wasan Gasar Firimiya a kakar bana
Jigawa First Lady Urges Northern Women to Embrace Entrepreneurship for Self-Reliance
Sakon Kungiyar Hamas ga Mutanan Duniya!!!
Turkiyya ta yi tur da harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a Qatar
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?