- Fiye da mutum 50 sun mutu bayan Isra’ila ta zafafa hare-hare a Gaza
Aƙalla mutum 50 ne aka ruwaito sun mutu a Gaza sakamakon ci gaba da hare-haren jiragen saman Isra’ila da dare, in ji hukumar agajin gaggawa ta Hamas.
Wannan na zuwa ne bayan mutuwar fiye da mutum 120 a yankin a jjiya, ranar Alhamis.
Halin da ake ciki na jin kai a Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa, yayin da Isra’ila ke ci gaba da hana shigar abinci da magunguna da sauran kayan agaji tun daga tsakiyar watan Maris.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana damuwarsa kan yadda halin jin ƙai ke kara tsananta a Gaza. Ya ce gwamnatin Trump “na cikin damuwa” kan halin da ake ciki.
Wannan ya sha banban da yadda yake mayar da martani a baya, inda sau da yawa yake kiran ƙungiyar Hamas da ta mika wuya maimakon bayyana damuwa game da rayukan fararen hula na Falasɗinu.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




