Rom Barslavsky Sojan Isra’ila Daya daga Wadanda Akayi Garkuwa da su a Gaza Ya Nuna Damuwasar na Yadda Yake Fama da Yunwa
A cikin wani faifan bidiyo da Saraya al-Quds ta watsa, na wadanda suka yi garkuwa da su daya daga cikin su wato Sojan Isra’ila Rom Barslavsky da ake tsare da shi a Gaza ya ce: – “Ba na ci kuma ba na sha. Don Allah a kawo abinci, saboda yunwa nake ji kamar zan mutu. Ina tsoron ba zan iya fita daga Gaza da rai ba. Wannan aikin na “Gideon Wagons” ya hana mu abinci. Netanyahu yana da alhakin rashin lafiyata da jinina”.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




