By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yan Sandan Najeriya.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yan Sandan Najeriya.
News

Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yan Sandan Najeriya.

Attajdid
Last updated: 2024/07/25 at 9:15 PM
Attajdid Published July 25, 2024
Share
Sufetan Yan sanda
SHARE

Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yansandan Najeriya.

Babban sufeton ‘yansadan Najeriya ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar zanga-zangar da wasu ‘yan ƙasar ke shiryawa a wata mai zuwa, yana mai cewa “za mu kare masu zanga-zanga matuƙar dai ta lumana ce”.

Sai dai da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar na faɗin Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi kira ga matasa da haƙura da zanga-zangar “saboda gwamnati na bakin ƙoƙarinta”.

Sufetan Yan sanda

“Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu zanga-zangar. Ba mu adawa da zanga-zangar lumana, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu ne” in ji shi lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

“Amma kuma akwai alhaki a kanmu na kare rayuka da dukiyoyi. Ba za mu zauna muna kallon ‘yandaba suna ƙona gine-gine da sunan zanga-zanga ba, ba za mu yarda da wannan ba.”

Ya ƙara da cewa sun samu bayanan yadda wasu ke kiran matasa su kwaikwayi irin zanga-zangar da mutanen Kenya suka yi “kwabo da kwabo” a Najeriya.

“Ina amfani da wannan damar na yi kira ga matasan Najeriya, don Allah ku yi watsi da kiran duk wanda ke neman ku fito ku tayar da hankali. Tuni Najeriya ta ɗanɗana matsalolin mummunar zanga-zanga.”

Matasa na cigaba da tattaunawa game da zanga-zangar da masu shirya ta suka ce za a yi daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, musamman a shafukan sada zumunta.

Shi ma Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar “su dakata tukunna har sai sun ji irin martanin zai mayar game da koke-kokensu”.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid July 25, 2024 July 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Video

Bayani kan Masjidul Aqsah tare da Malam Aminu Aliyu Gusau.

Attajdid Attajdid August 3, 2024
Rasha da Ukraine Sun Amince da Musayar Fursunonin Yaƙi
An Kaiwa Jagororin Kungiyar Hamas Hari a Doha
Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso 
Another Tanker Explosion Along Jigawa/Kano Boader with No Casualties
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?