Rasha da Ukraine Sun Amince da Musayar Fursunonin Yaƙi
An fara tattaunawa tsakanin Turkiyya da Amurka da Ukraine a Fadar Dolmabahce da ke Istanbul.
Daga cikin waɗanda ke halartar tattaunawar akwai Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da tawagar Amurka ƙarƙashin jagorancin Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio da Ministan Tsaron Ukraine Rustem Umerov.
Rasha da Ukraine sun amince su yi musayar fursunonin yaƙi 1,000 kowannensu wanda shi ne musayar fursunoni mafi girma tun da aka fara yaƙi, kamar yadda ministan tsaron Ukraine ya bayyana.
An cim ma yarjejeniyar ne yayin da tattaunawar da Turkiyya ta shirya a Istanbul tsakanin wakilan Rasha da na Ukaraine.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




