Harin Isra’ila a Doha
Isra’ila ta kai wani mummunan hari a birnin Doha. Shugaban majalisar Isra’ila – Knesset – ya bayyana cewa wannan hari sako ne ga dukkan Gabas ta Tsakiya.
Martanin Hamas
Daga ɓangaren Hamas, ɗan majalisar siyasa na ƙungiyar, Dr. Suhail al-Hindi, ya tabbatar da cewa harin ya auku ne yayin da tawagar masu tattaunawa ke taro kan shirin Amurka.
Ya ce jinan shugabannin Hamas ba su fi darajar na sauran Falasɗinu ba, kuma duk da yunƙurin kisan gilla, shugabannin sun tsira.
Sai dai akwai shahidai da dama ciki har da Jihad Lubad da Humam Khalil al-Hayya.
Alƙawarin Hamas
Hamas ta ce: “Ba za mu ɗaga farin tuta ba, ba za mu ajiye makamai ba. Za mu ci gaba da yaƙar mamaya da duk ƙarfinmu.”
Martanin sauran ‘yan siyasa
A nasa jawabin, sakataren janar na ƙungiyar Mubadara al-Waṭaniyya, Mustafa Barghouthi, ya yi gargadin cewa wannan hari na Doha zai iya zama juyin-juya hali mai tsananin tasiri. Ya ce lamarin zai iya shafar Isra’ila gaba ɗaya tare da Firayim Minista Netanyahu da sauran shugabanni.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama
At-tajdid News.




