Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Nijeriya, Ulama Forum ta bayyana rashin amincewarta da ƙudurin yi wa haraji garambawul wanda Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya aika wa majalisa don amincewa da shi.
A wata sanarwa da majalisar malaman ta fitar a ranar Litinin, mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Aminu Inuwa Muhammad da sakatarenta Injiniya Basheer Adamu Aliyu da wasu malaman 23 suka sanya wa hannu, sun ce wasu tsirarun jihohi ne za su fi cin moriyar mafi yawan kuɗaɗen harajin da za a riƙa tarawa a sabon tsarin.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




