Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
Liverpool da Real Madrid na gogayya kan kan dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz, Arsenal ta bayyana kudin sayen dan wasan gaba na RB Leipzig Benjamin Sesko, yayin da Manchester United da Chelsea ke neman dan wasan gaban Ipswich Liam Delap.
Real Madrid na yunkurin dauko dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz duk da cewa dan wasan na Jamus mai shekara 22 yana da ra’ayin komawa Liverpool. (AS Spanish)
Brentford ta tuntubi Liverpool kan sayen golan Jamhuriyar Ireland Caoimhin Kelleher, mai shekara 26, kan fam miliyan 20. (Liverpool Echo)
Yunkurin na daukar Kelleher ya zo ne a daidai lokacin da Brentford ke shirin barin golan Holland mai shekara 31 Mark Flekken ya koma Bayer Leverkusen. (Independent)
Bayern Munich na sha’awar sayen dan wasan gaban Liverpool Cody Gakpo, mai shekara 26, inda kulob din Bundesliga ke daya daga cikin kungiyoyi uku da dan kasar Netherlands din ke son komawa. (Florian Plettenberg)
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




