Falasɗinawa suna yin sallar jana’iza ga wasu ‘yan uwansu da aka kai Asibitin Nasser bayan kisan da Isra’ila ta yi musu a harin da ta kai birnin Rafah.
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani hari ta sama da Isra’ila ta kai a wata makaranta a tsakiyar Gaza ya ƙaru zuwa 22, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin.
Ya ƙara da cewar sojojin Isra’ila “suna sane cewa dubban mata da yara da aka kora daga gidajensu suna samun mafaka a makarantar ta Mufti amma suka kai mata hari da bama-bamai.”
Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce akwai buƙtatar Isra’ila ta daina amfani da ƙarfin soji kana ta rungumi hanyar diflomasiyya a yaƙin da take yi a Lebanon.
Da yake magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant, Austin ya ce ya aika ta’aziyyarsa bisa mutuwar sojojin Isra’ila a wani hari na jirgi mara matuƙi da Hezbollah ta kai musu.
“Na jaddada buƙatar tabbatar da tsaron lafiyar (Dakarun Wanzar da Tsaro na MDD a Lebanon) UNIFIL da Sojojin Lebanon da kuma buƙatar mayar da hankali kan sulhu ta hanyar diflomasiyya da daina amfani da ƙarfin soji,” in ji shi a saƙon da ya wallafa a shafin X.
Rundunar sojojin Isra’ila ta ce sojojinta huɗu sun mutu sakamakon harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi a sansaninsu da ke kudancin Haifa.
“An kashe sojoji huɗu na IDF a harin, sannan guda bakwai sun yi mummunar jikkata,”a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar.
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra’ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.
At-tajdid News.





