Amnesty, Da Likitocin England Sun Bukaci Israel Ta Saki Maaikatan Lafiya Palestine 95
Kungiyar Karen Hakkin Dan”Adam da ta Likitocin Kasar Birtaniya sun Bukaci Kasar Israel da ta gaggauta sakin ma”aikatan Lafiya Palasdinawa sama da 95 da ke tsare a gidajen yarim Kasar.
Kungiyoyin sun yi wannan Kiran ne ya yin wata zanga-zangar da su ka gudanar a Dandalin St.Thomas’ Hospital da ke tsakiya Birnin London
Al-Jazeera ta rawaito cewa daga cikin wadanda ke tsare a kurkukun na Israel har da Hussam Abu Safia Daraktan Asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza.
Kungiyoyin sun bayyana tsare maaikatan lafiya tare da gallaza musu a matsayin wani laifi na keta hakkin Dan”Adam da kuma laififfukan Yaki wadda duniya ke Allahwadarai da Shi.
Isra’ila ta Kama Maaikatan Lafiya da ke aiki a yankin Gaza guda 431 in da ta Saki 309 bayani yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanyawa hannu.
A cikin ya kin shekaru biyu da Israel ta kaddamar a Gaza ta kashe maaikatan Lafiya Sama da 1,700 ta kuma lalata Kashi 95 na cibiyoyin Kiwon Lafiya a yankin.
Tuni dai Kotun Duniya ta bayyana shugaban Israel Benjamin Natanyaho A matsayin wadda ta bada sammacin kamowa sabo da laififfukan Yaki.
Zuwa yanzu Isra’ila ta kwashe mutanen sama da 65,000 a Gaza ciki mafia yawa Mata da kananan Yara, tare da kuma hana shigar da kayan a gaji da magunguna yankin da ta wargaza Sakamakon ruwan bamabamai da ta ke yii




