Rundunar sojin Isra’ila ta sanar da kashe sojoji uku a wani harin bam da aka kai tare da raunata wasu uku ciki har da wani jami’i a arewacin Gaza, kuma kafafen yada labaran yahudawan sun ce lamarin ya faru ne sakamakon fashewar na’urorin masu fashewa da aka dasa a kan wata tanka.
A wani Video da Mayakan Al-Qassam Brigades suka nuna a shafinsu ya nuna wata arangama da suka yi da dakarun Isra’ila a yayin da suke kutsawa cikin Jabalia dake arewacin zirin Gaza, tare da kwace wasu jiragen yaki marasa matuka.
Al-Qassam Brigades sun bayyana nauyin dake kansu na kara samar da hadin gwiwar rundunonin Quds Brigades da na Shahidaiq Al-Aqsa, kan harin da aka kai a kauyen Al-Funduq da ke Qalqilya.
Al-Qassam ta yabawa Kwamanda Jaafar Dababssa, shi ne ya shirya wannan kokari da jarumta da juriyar aikin wanda ya isar da sakon hadin kai mai karfi da kuma ayyukan haɗin gwiwar da ke tafe za su kasance mafi kyawun saƙon jituwa tsakanin ƙungiyoyin ta fuskar duk wanda ke neman kai hari. Aljazeera.
Mai rahoto;
M.B.Gama.
At-tajdid News.




