By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Trump ya Nuna Shakku Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Trump ya Nuna Shakku Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza
International News

Trump ya Nuna Shakku Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza

Attajdid
Last updated: 2025/01/21 at 8:36 AM
Attajdid Published January 21, 2025
Share
SHARE

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na uku bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a yankin da ya kashe  Falasɗinawa fiye da 47,035, ciki har da wani yaro da ta kashe a Rafah da kuma sace gomman mutane a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

 

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shakkunsa game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza a yayin da aka tambaye shi kan ko yana da ƙwarin gwiwa game da yiwuwar aiwatar da dukka matakai uku na yarjejeniyar.

 

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a ofishin shugaban ƙasa bayan sanya hannu kan dokokin shugaban ƙasa, Trump ya ce yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya ya yi kama da “wani babban wuri da aka rusa” kuma ya kamata a sake gina shi a wani tsari na daban.

 

Shugaban Amurka Donald Trump ya soke takunkuman da tsohuwar gwamnatin Biden ta ƙaƙaba wa Isra’ilawa ‘yan kama-wuri-zauna bisa musguna wa Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda sabon shafin intanet na Fadar White House ya bayyana.

 

Shafin ya ce Trump ya soke Dokar Shugaban Ƙasa mai lamba 14115 wadda aka amince da ita ranar 1 ga watan Fabrairun 2024, wacce kuma ta amince a sanya takunkumai kan “mutanen da ke yin tarnaƙi game da zaman lafiya da tsaron Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.” TRT African Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

 

At-tajdid News.

 

 

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid January 21, 2025 January 21, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SHUGABA TINUBU YA BAYYANAWA ‘YAN NIGERIA AKN ZANGA-ZANGAR

Attajdid Attajdid August 4, 2024
YARA MANYAN GOBE: A RANAR YARA TA DUNIYA DAGA FADAR SARKIN KATSINAN GUSAU, ALH. DR. IBRAHIM BELLO.
GOBARA TA BARKE A SANSANIN YAN GUDUN HIJIRA NA ROHINGYA
Shugaba Paul Biya ya Koma Kamaru Bayan Shafe Makonni ba ya nan
Hisbah Aikin Allah: Gwamna Amadu, Gwamnan Addini.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?