Jiragen yaƙin Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya sun halaka ’yan ta’adda da ke shirin kai sabon hari kan babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna da ke ƙoƙarin gyarawa.
Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu a hannun sojoji ne a ranar Juma’a, a yayin da ma’aikata ke ƙoƙarin gyara babban layin lantarkin da ke ɗauko lantarki daga Babbar Tashar Shiroro, ya raba wa yankin Arewa.
Kakakin rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Iya Komodo Olusola Akinboyewa, ya ce an halaka su a Dajin Alawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu




