Real Madrid ta amince da biyan Fam Miliyan 50 ga Dan wasa Dean Huijsen
Real Madrid na daf da ɗaukar ɗan wasan baya na Bournemouth Dean Huijsen bayan gama cinikinsa kan fam miliyan 50.
Ɗan wasan na Sifaniya zai zama ɗan wasa na biyu da Real za ta ɗauka don shirya wa kaka mai zuwa bayan ta ɗauki Trent Alexander Arnold na Liverpool.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




