By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Wani Fitaccen Malamin Addini ya Soki Gwamna Dauda Saboda Gazawa Wajen Magance Tsaro a Zamfara
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Wani Fitaccen Malamin Addini ya Soki Gwamna Dauda Saboda Gazawa Wajen Magance Tsaro a Zamfara
News

Wani Fitaccen Malamin Addini ya Soki Gwamna Dauda Saboda Gazawa Wajen Magance Tsaro a Zamfara

Attajdid
Last updated: 2024/11/10 at 6:15 PM
Attajdid Published November 10, 2024
Share
SHARE

A cikin tsokaci mai tsanani kan mummunan rashin tsaro da ake fuskanta a Jihar Zamfara, fitaccen malamin addinin Musulunci Farfesa Mansur Sokoto ya bayyana a fili yadda Gwamnan Dauda Lawal ke gudanar da lamuransa, yana zargin cewa ya yi sakaci da nauyin da ke kansa kuma yana daura laifin ga wasu mutane Daban.

 

A cikin wani bidiyo na baya-bayan nan, Farfesa Sokoto tare da wasu malaman addini, sun kira gwamnan da ya dauki mataki mai karfi kan hare-haren ‘yan ta’adda da ke ci gaba da kashe rayuka da korar al’ummomi daga mazaunansu.

 

Matsalar tsaro a Zamfara ta kasance.matsala mai muni, Wadda kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da masu tsattsauran ra’ayi Fulani, suke kai hare-hare suna kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba. Adadin kisan gillar ‘yan ta’adda a Najeriya ya kasance mai girma, inda aka kiyasta rasuwar mutane 4,020 a cikin watanni goma na farkon shekarar 2022.

 

Sokoto ya jaddada cewa Gwamnan Lawal, ya san da rikicin tun kafin lokacin da ya hau kan karagar mulki, Don haka ba Wani uzuri dole Gwamnan ya nuna shugabancin da ake bukata wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar. Duk da kokarin Lawal na baya-bayan nan na kafa Asusun Tsaro na Jihar mai mambobi 21 da halartar tattaunawar tsaro ta yankin, Sokoto ya nace cewa wadannan matakai basu isa ba wajen samar da cikakkiyar Mafita da ake bukata gaggawar magance kalubalen Matsalar Tsaron Zamfara shi ne mafi aala fannoni.

 

Mutanen Zamfara, da suka tsinci kansu a tsaka mai wuya da karuwar tashin hankali, suna bukatar a dauki matakin da ya dace, ba kawai maganganu ba. Sokoto ya jaddada cewa lamarin na bukatar cikakken lissafi daga Gwamnan Lawal don fifita jin dadin da tsaron mutanensa.

 

“Ya kamata ka daina zargi da kukawa game da wanda ya rike mukamin kafin ka. Idan kuka ya yi yawa, za a iya daukarka a matsayin mace,” in ji Sokoto.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid November 10, 2024 November 10, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Mai kwashe sharar da ya shekara 40 yana tara kuɗin Hajji ya isa Saudiyya tare da matarsa

Attajdid Attajdid May 24, 2025
Sarkin Musulmi ya Bayyana Dalilin da ya sa Ake Ganin Kamar Sarakuna na Tsoron Gwamnoni
Akalla An Sami Mutane 30 Sun Mutu a Ambaliyar Ruwan data Barke a Jahar Maiduguri.
Kotu Ta Tasa keyar Wani  Alƙalin Bogi Gidan Gyaran Hali a Kano
Majiya daga Isra’ila:Ta tabbatar da an kai sojoji 10 zuwa 15 zuwa asibitoci
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?