Kwamishinan sufuri na jahar Kano Ibrahim Namadi ya sauka daga Mukaminsa sa’oi kadan bayan gwamnan kano Abba kabir yusuf ya karbi rahoton kwamitin bincike kan tsoma hannu da Kwamishinan ya yi wajen karbar belin suleman Danwawu da ake zargi da safarar kwayoyi.
Namadi ya bayyana saukarsa daga mukaminne a wata sanarwa da Daraktan sadarwa da hulda da Jama’a na gwamnatin kano ya fitar.
A cewar Namadi matakinsa na sauka daga kujerarsa na da nasaba da bukatar al’umma da kuma yanayin zarge-zargen da ke kansa.
Tsohon kwamishinan na Sufuri ya godewa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf a saboda ba shi damar da ya yi na ya Hidimtawa jahar kano tare da jaddada aniyarsa ta cigaba da martaba Jagoranci da kuma shugabanci nagari.
Sanarwar ta ce gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya karbi takardar saukar kwamishinan daga mukaminsa tare da yi masa fatan alheri a al’amuransa anan gaba.
Mai Rahoto
Nura Abubakar Musa




