By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Idan Isra’ila Ta Samar da Iron Dome Turkiyya Zata Samar da Steel Dome, (Rumfar Ƙarfe)” Inji Shugaba Erdogan
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Idan Isra’ila Ta Samar da Iron Dome Turkiyya Zata Samar da Steel Dome, (Rumfar Ƙarfe)” Inji Shugaba Erdogan
International News

Idan Isra’ila Ta Samar da Iron Dome Turkiyya Zata Samar da Steel Dome, (Rumfar Ƙarfe)” Inji Shugaba Erdogan

Attajdid
Last updated: 2024/09/02 at 7:05 AM
Attajdid Published September 2, 2024
Share
SHARE

Turkiyya ta shirya don bunƙasa aikinta na tsaron sama “Steel Dome” kamar yadda Shugaba Erdogan ya bayyana, yana fatan haɗe tsarin tsaron sama da abubuwan da ke gano motsi da makamai, yayin da take ƙara inganta ƙarfinta a ɓangaren jirage marasa matuƙaBunƙasar Turkiyya a shirinta na samar da jirage marasa matuƙa na daga muhimman nasarorinta a ɓangaren soja.

Shugaban Turkiyya ya bayyana a ranar Asabar cewa ƙasarsa za ta gudanar da aikinta na tsaron sararin samaniyar “Steel Dome” (Rumfar Ƙarfe).”Muna fata za mu gudanar da aikinmu na ‘Steel Dome’ (Rumfar Ƙarfe) da duka abin da ya ƙunsa.

Idan su (Isra’ila) suna da Iron Dome, mu ma za mu yi Steel Dome,” kamar yadda Recep Tayyip Erdogan ya faɗa a wajen Bikin Ƙaddamarwa da Miƙa Tuta a Kwalejin Yaƙi ta Sama.

Steel Dome zai tabbatar da cewa matakanmu na tsarin kariya ta sama da duka na’urorinmu masu gano motsi da makamai suna aiki tare da juna,” a cewar Erdogan.

Erdogan ya jaddada ƙara shaharar Turkiyya a ɓangaren fasahar jirage marasa matuƙa.”Ana sa ido da ƙyashi kan nasarar da muka cim ma a ɓangaren jirage marasa matuƙa, ba wai kawai daga ƙasashe abokanmu da ‘yan’uwanmu ba, har ma daga ko ina a duniya,” a cewarsa.

Idan aka ƙaddamar da jirage marasa matuƙa na Kizilelma and ANKA-3, waɗanda ake ci gaba da gwada su, Turkiyya za ta zama wacce ake damawa da ita a wani “sabon rukuni” a wannan ɓangaren, kamar yadda Erdogan ya bayyana.Yaƙi da Ta’addanciShugaban na Turkiyya ya kuma nanata aniyar Turkiyya ta inganta ƙarfinta na soji, yana mai cewa: “Muna ƙoƙarin ƙerawa da bunƙasawa ko kuma sayo duk wani abu da rundunar sojin samanmu ke buƙata, tun daga makamai masu linzami zuwa na’urorin kariya ta sama.”

“Rundunar sojin samanmu na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta wajen kawar da barazana ga tsaron ƙasarmu, musamman a yaƙi da ta’addanci,” inji shi.

Da yake magana game da ci gaba da Operation Claw-Lock, wanda aka ƙaddamar a shekarar 2022 don kai hari kan maɓoyar ‘yan ta’addar PKK a arewacin Iraƙi, Erdogan ya ce za su tabbatar da cewa ‘yan awaren sun daina zama wata barazana ga “al’ummarmu da ‘yan uwanmu na Iraƙi.

“Erdogan ya ce wasu ƙawayen, maimakon goyon bayan Turkiyya, ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna goyon bayansu ga ƙungiyar ta’addanci ta PKK a Siriya da kuma kyakkyawar maraba ga jagororin ƙungiyar ta’addanci ta ‘yan aware.

Ya ƙara da cewa “Muna dogara ne kawai da karfinmu da jajircewarmu.”Erdogan ya kuma yaba wa dakarun Turkiyya dangane da shawo kan ƙalubalen da suka fuskanta da suka haɗa da juyin mulkin da ƙungiyar ta’addanci ta Fetullah ta shirya a shekarar 2016.

“Ba wai kawai mun tumɓuke ƙungiyar ta’addanci ta FETO da ta yi girma kamar muguwar cuta sankara kusan shekaru 40 ba, mun kuma ƙarfafa sojojin mu a kowane fanni,” in ji shi.Shugaban ya ce Turkiyya na haɗin kai da “abokanta da ‘yan uwanta a duk inda ake buƙata.

“Ankara na goyon bayan ƙawayenta a Libya da Somalia da Azarbaijan.

Shugaban ya ce babu wani soja a duniya, in ban da rundunar sojan Turkiyya, da za ta iya samun irin wannan nasarar fiye da iyakokinta cikin ƙanƙanin lokaci.TRT AFRIKA HAUSA.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 2, 2024 September 2, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
Books & Journal

TAJADIDIN SHEHU DAN FODIYO – TABBATAR DA ADDINI, NEMAN MULKI, KO KABILANCI? (1) SHEIKH AMINU ALIYU GUSAU

Attajdid Attajdid May 17, 2025
Ranar Yara ta Duniya 
LABARAN HALIN DAKE CIKIN A GAZA DA GABAS TA TSAKIYA
An Kashe Sama da Mutane 53600 a Palestine 
Sojojin Isra’ila Sun Shahadantar da Muhammad Jaber  “Abu Shuja” .
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?