Kamfanin yada labarai na Al-Jazeera ya yi Kira ga Yanjarida, da lauyoyi, da sauran hukumomin kare hakkin Dan”Adam na Duniya da su kaiwa “Yanjaridar Gaza dauki sakamakon yunwa da Kisan gillar da suke fuskanta da .
Yanayin da suke ciki ya biyo bayan Kisan kiyashi, da takunkumin Yunwa da Israila ta kakabawa yankin wadda ya shafe watan 21.
Kamfanin ya nuna damuwarsa Kan yanayin da Yan”jarida da sauran mutanen wanna yaki ke ciki, ya kuma bayyana cewa tarihi ba zai yafe ma duk mutumn da ke raye a Yanzu ba idan aka gaza yin aiki don kawao karshen wanna taaddancin da ke faruwa ba.
Kamfanin ya yabawa sadaukarwar da Yanjarida ke yi a Gaza, wadda izuwa Yanzu dayawa an kashe su wasu kuma an jikkatasu, Amma sauran na cigaba da rike amanar aikin.
A cewar wani babbaban Jami”i maikula da sashin fusahar AI, Mustafa Saoug I dan ba a tashi state an dauki kwakkwaran mataki ba to nan gaba kadan za”a rasa wadanda zasu bada labarin mummunan halin da ake ciki a yankin.
Kasar Israila ta kaddamar da yaki a yankin na Gaza wadda izuwa Yanzu da kashe Sama da mutum 60,000 mafi yawa Mata da kananan yara.
Haka kuma ta sanyawa yankin takunkumin Yunwa ta hanyar ana shigar da kayan abinvi da na again jinkai cikin yankin na Gaza.
Mairahoto
Muhammad Garba
At’tajdid News




