Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid: –
Yana cewa Erdogan ya sake yin kaca-kaca kuma hakan yana haifar da hadari a Gabas ta Tsakiya kuma dole ne duniya, musamman kungiyar tsaro ta NATO, ta yi Allah wadai da barazanar da Erdogan ke yi wa Isra’ila tare da tilasta masa ya daina goyon bayan Hamas.

Wakilin Aljazeera:
Ya bayyana dakarun mamaya sun mamaye garin Jama’in da ke kudancin Nablus inda suka kai farmaki kan wasu gidaje.
Wakilin Aljazeera:
Ya bayyana cewa tankokin Isra’ila sun kai hari a unguwar Sheikh Nasser da ke birnin Khan Yunus a kudancin zirin Gaza.
Muhannad Mustafa:
Yana cewa “Isra’ilawa sun yi imanin cewa shawarwarin Netanyahu za su kawo cikas ga ci gaba da tattaunawar da akeyi akan yakin Gaza.
Jiragen saman mamaya sun kaddamar da wasu jerin samame a yankuna daban-daban a birnin Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.

Adadin hare-haren da aka kai a Khan Yunis cikin sa’o’i 48 a Gaza sun kashe kimanin mutane 129.
An sami shahidai 3 da jikkata yara da dama sakamakon harin bam da Isra’ila ta kai a wani gida da ke unguwar Al-Sabra da ke kudancin birnin Gaza.
A wani hari da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira an samu shahidai da raunuka a harin bam da ta kai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a Mawasi Khan Yunis zuwa yanzu ba a iya tantance wadanda suka yi shahadaba da kuma raunuka. Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




