Rahotanni daga jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, na cewa ambaliyar ruwa ta mamaye garin Bindigi da ke karamar hukumar Fune inda ta lalata gidaje akalla 50, da gonaki.
Kazalika ambaliyar ta kuma yi awon gaba da dabbobi da dama.
Tuni dai mutanen garin da dama da ambaliyar ta afkawa suka koma wata makaranta da asibiti inda suka samu mafaka.
Yanzu haka dai jama’ar garin na Bindigi na can cikin halin kaka-nika-yi sakamakon afkuwar ambaliyar ruwan da ta mamaye garin.
Wani mazaunin garin da BBC ta tattauna da shi ta wayar tarho, Bulama Alhaji Audu, ya ce ambaliyar ruwan ta wuce yadda ake tsammani.
Ya ce, “Ambaliyar ruwan ta kusa shafe garin baki daya, kuma ba karamin ta’adi ta yi ba domin duk gidajen laka sun rushe, to amma ba a yi asarar rai ba, saboda mutane sun ankara da wuri duk bar gidajensu.”
Bulama Alhaji Audu, ya ce akwai dabbobi da yawa da suka bi ruwa, sannan ko bacci mutanen garin basa yi saboda gudun kada wani mummunan abu ya faru cikin dare.
Mutanen garin na Bindigi dai na matukar bukatar taimakon gaggawa.
A nata ɓangaran kamar yadda majiyarmu ta bayyana mana, gwamnatin jihar ta Yobe ta ce tana kokarin kai daukin gaggawa garin da ma sauran wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Dakta Muhammad Goje, shi ne shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ya shaida wa BBC cewa, ko shakka babu sun samu labarin abin da ya afku na ambaliya, ba a Bindigi kadai ba har ma da wasu wurare.
Ya ce, “Tuni gwamnan jihar ya bayar da umarnin aje wuraren da ambaliya ta afku don a tantance irin ɓarnar da ta yi domin kai ɗaukin gaggawa.”
“Bindigi na daga cikin garin da za a kai daukin gaggawa, domin a karamar hukumar Fune da Bindigin ke ciki na kai daukin gaggawa garuruwa takwas.”
Shugaban hukumar agajin gaggawan, ya ce yanzu za a kai kayan da ake sanyawa idan za a shiga kwale-kwale domin akwai wuraren da sai dai a rinka tsallake ruwa da kwale-kwalen.
Ya ce, “Ga wadanda suka fake a gine-ginen gwamnati kamar makarantu da asibitoci na kai wa wasu a garuruwa da dama kayayyakin masarufi da kuma kayan kariya daga wasu cutuka.”
“In sha Allahu Bindigi ne gari na gaba da za a kai wa kayan ɗauki kamar na masarufi da sauransu.”
Tun cikin watan Agustan da ya gabata mamakon ruwan sama ke ci gaba da haifar da gagarumar ambaliya a sassan Najeriya, al’amarin da ya jefa dubban mutane cikin tsaka mai wuya, kuma ya raba su da muhallansu, baya ga lalata gonaki da kayan amfanin gona da dai sauran su.
Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta yi hasashen cewa za a samu mamakon ruwan sama a kwana biyar masu zuwa kuma zai iya janyo ambaliyar ruwa a wurare 123 na jihohi 21 na ƙasar.
Rahoton ya bayyana jihohin Benue da Kogi da Anambra da Delta da Rivers da Imo da Bayelsa a matsayin jihohin da iftila’in zai fi ƙamari.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa wani rahoto da hukumar kare muhalli ta fitar ya yi kira ga mazauna waɗannan jihohi su riƙa sanya idanu tare da lura da al’amura.
At-tajdid News.




