Likitocin Falasdinawa sun gano gawawwakin Falasdinawa 53 daga karkashin baraguzan gine-gine a Gaza, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a yankin tun daga watan Oktoban 2023 zuwa 47,161, in ji ma’aikatar lafiya.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kuma kwantar da mutane 19 da suka jikkata a asibitoci cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin wadanda suka jikkata zuwa 111,166 a harin da Isra’ila ta kai.
“Mutane da yawa har yanzu suna makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto ba su iya isa gare su,” in ji ta.
Sojojin Isra’ila sun kashe wani Bafalasɗine magidanci a gaban matarsa da ‘ya’yansa uku yayin da yake tuƙa mota a birnin Jenin citda ke arewacin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kutsawa yankin.
Wani bidiyo da iyalan mutumin suka ɗauka wanda aka riƙa watsawa a shafukan intanet ya nuna mawuyacin halin da Ahmed Nimer Obeidi Shayeb lokacin da aka harbe shi.
A yayin da yake tattaunawa da Anadolu Agency, Bashir Matahen, Daraktan Watsa Labarai na Birnin Jenin, ya ce Ahmed Shayeb yana tare da iyalansa matarsa da ‘ya’ya uku suna hanyar komawa gida yayin da wani sojan Isra’ila gwanin harbi daga ɓoye ya buɗe masa wuta.
A gefe guda, Matahen ya ce Falasɗinawa fiye da 600 sun tsere daga sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin a yayin da dakarun Isra’ila suke ci gaba da kutsawa birnin na Jenin.
Isra’ila ta ƙaddamar da jerin hare-hare a birnin Jenin na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla tara da jikkata aƙalla mutum 40, in ji jami’in kiwon lafiyar Falasɗinu, a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta ƙulla da Hamas ta shiga kwana na huɗu a Gaza.
A Tel Aviv, an jikkata mutum huɗu a wani hari da aka kai musu da wuƙa ko da yake jami’an tsaro sun kashe mutumin da ya kai harin, a cewar ‘yan sandan Isra’ila.
Hukumomi sun ce mutumin da ya kai harin “ɗan ƙasar waje” kuma yana da shekaru 28 suna masu cewa harin na ta’addanci ne. TRT African Hausa.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News




