By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Kano ta haramta bikin ‘ƙauyawa day’ da soke lasisin gidajen bukukuwa
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Kano ta haramta bikin ‘ƙauyawa day’ da soke lasisin gidajen bukukuwa
NewsUncategorized

Gwamnatin Kano ta haramta bikin ‘ƙauyawa day’ da soke lasisin gidajen bukukuwa

Attajdid
Last updated: 2025/05/17 at 9:58 PM
Attajdid Published May 17, 2025
Share
SHARE

 

Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Abba El-Mustapha ya ce sun samu ƙorafi daga jama’ar gari da malamai da ‘yan kasuwa wanda hakan ya sa aka haramta wannan biki.

Shugaban hukumar kuma ya gargaɗi masu ɗora abubuwa a kafafen sada zumunta inda ya ce dokar ta ba su damar sa ido kan abubuwan da jama’a ke ɗorawa musamman na nishaɗi. / Others

5 awanni baya

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta haramta bikin ƙauyawa day da kuma soke lasisin duk wani gidan gudanar da bukukuwa ko kuma event center a jihar.

 

Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Abba El-Mustapha ne ya sanar da hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Asabar.

 

Wannan na zuwa ne a yayin da mutane da dama ke ƙorafi a shafukan sada zumunta game da shiga ta rashin kamala da wasu mata ke yi a lokacin bikin.

 

Shugaban hukumar ya ce sun samu ƙorafi daga jama’ar gari da malamai da ‘yan kasuwa wanda hakan ya sa aka haramta wannan biki.

 

Ya kuma ce tuni suka yi haɗin gwiwa da jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da ‘yan sanda da hisbah da sauran jami’a domin aiwatar da wannan doka.

 

Haka kuma Abba El-Mustapha ya bayyana cewa sakamakon gyaran dokar hukumar tace fina-finai da majalisar dokokin ta Kano ta yi wadda gwamnan jihar ya saka wa hannu, sun soke lasisin duk wata event center a jihar inda ya ce ya zama tilas duka irin waɗannan gidaje a Kano su je su sabunta rajistarsu.

 

Haka kuma ya bayyana cewa sabuwar dokar ta haramta ɗora fina-finai a soshiyal media har sai hukumar ta tace su.

 

Shugaban hukumar kuma ya gargaɗi masu ɗora abubuwa a kafafen sada zumunta inda ya ce dokar ta ba su damar sa ido kan abubuwan da jama’a ke ɗorawa musamman na nishaɗi.

 

Ya kuma ce a yanzu dokar ta ba su dama su sa ido kan masu gidajen hoto da gidajen buga takardu da masu zane da masu aikin MC a gidajen biki da kuma masu wasanni a kan titi.

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

At’tajdid News

You Might Also Like

Jigawa NSCDC: 125 Prosecutions, 9,000 Guards Trained in 2025

Jigawa NUT Gets New Executive

Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa

Jigawa Anti-Corruption Commission Decries Legal Delay , Recorded 479 Cases , in 2025

Pressure Mounts on Sule Lamido To Quiet PDP

Attajdid May 17, 2025 May 17, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

An tallafawa Wadanda Ambaliyar Ruwa ta Shafa a Jahar Jigawa.

Attajdid Attajdid August 26, 2024
Leadership Award: : Celebrating Namadi”s purposeful Leadership 
Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
April 1, 2025
Jigawa Congratulates New APC National Chairman 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?