Jiya nayi alkawarin zan tofa albarkacin bakina akan wasu kudurorin dokoki da shugaba Bola Ahmed Tinubu.ya gabatarwa majalisar dokoki ta kasa. An gabatar da wadannan dokoki don a yi wa fasalin harajin kasa garanbawul.
Wasika PBAT ya aikewa shugaban majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio kwafinsa. Sannan aka aikewa shugaban majalisar wakilai Dr Tajuddin Abbas nasa kwafin. A bisa ka’idar aikin majalisun za a zo da takardar gaban ‘yan majalisa a daga murya a karanta kowa ya ji. Idan an karanta shi ne abin da ake cewa ” An yi karatun farko wato First Reading.
Tun kafin a zo nan wajen a ranar 30 ga watan Oktoba 2024 a wani zama na majalisar tattalin arziki ta kasa, National Economic Council, wannan zauren ya kunshi duk gwamnoni na jihohi 36 da kuma ministan Abuja. Haka majalisar ta kunshi gwamnan babban banki CBN da minstocin kudi da kasafi da tsare-tsare, kuma shi wannan zauren yana karkashin mataimakin shugaban kasa. Atiku Abubakar ya taba rikewa, Farfsea Yemi Osinbajo ya rike shi, yanzu kuma yana hannun Kashim Shattima. Kundin tsarin mulki shi ya baiwa mataimakin shugaban kasa wannan iko. Aikinsa kawai ya baiwa shugaban kasa shawara ta tattalin arziki, Amma aiki da shawarin ba lallai ba kuma tilas. A wannan zaman an gayyyaci Taiwo Oyedele, wato Chairman Presidential Committee on Fiscal Policy and Tax Reforms babban muhutin haraji kuma shugaban kwamitin Dabarun tara kudi da sarrafa su domin ya wayar da kan gwamnoni mai ke kunshe cikin maganar haraji. Haka an gayyyaci Zacceus Adedeji shugaban hukumar tara kudin haraji ta kasa wato FIRS duk a wannan rana. A wajen wannan zama ne aka zartar cewa a gaya wa shugaban kasa ya jingine wadannan dokoki har sai an sake duba su sarai, an yi shawara. Gwamnan jihar Oyo, wanda Bayerabe ne kuma dan jam’iyyar PDP Seyi Makinde shi ne ya yi magana a madadin duk gwamnoni.
Amma kuma tun kafin wannan ranar a karkashin kungiyar gwamnoni na arewa Northern Governors Forum NGF da manyan sarakunan yankunansu sun hada baki guri guda cewa ba su gamsu da akasarin tanadin da ke kunshe cikin wadannan sabbin dokokin da ake son zartaswa ba. A wannan taron da aka yi a Kaduna ranar 23 ga Oktoba 2024 gwamnan jihar Gombe, Alhaji Yahaya Inuwa dan jamiyyar APC shi ne ya fadawa duniya matsayin da suka dauka a dunkule.
Ai kuwa a yammacin ranar da NEC ta zauna ta ce a janye wannan kudurorin daga zauren majalisar har sai an yi kwaskwarima, Bayo Ononuga, mai baiwa shugaban kasa shawara akan labarai ya fito fili ya ce , duk wanda yake da wata magana ya tafi majalisar kasa, a can za a yi muhawara, duk inda ake da bukatar gyarawa a bi wannan tsarin sai a gyara. Kalmomin Bayo basu yi wa gwamnoni da sarakai da wasu shugabanni da ‘yan siyasa dadi ba. Nan da nan sai cece-kuce.
Magana ta gaskiya ita ce. Tun lokacin da aka tsayar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC ya yi kamfen kuma an bashi goyon baya ya dauki niyyar zai aiwatar da salon Mulki ta fuskar tattalin arziki da siyasa irin yadda ya yi a zamanin da ya mulki jihar Lagos. Don haka a ranar da aka rantsar da shi ya cire tallafin man fetir. A tsakanin kwana 30 kuma ya sakarwa Naira mara ta nemawa kanta daraja a tsakanin kudaden musaya na duniya. A cikin wata biyu kuma ranar 7 ga watan Yuli 2023 ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin shugaban kwamitin fasalin harkar kudi da gyara harajin Najeriya. A wannan lokacin ne kuma aka tabbatar da Zacceus Adedeji mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar haraji daga bisani kuma aka tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar FIRS. Su biyun nan, daya dan Lagos daya dan Ogun, sune suka tsara yadda za a tafiyar da haraji a kasar nan, bisa umarnin shugaban kasa. Sun shafe watanni 15 su hada nan, su kulla can, jama’armu kuma suna kwance a gida ko kuma sun can wata sharholiya.
A cikin aikin da suka gabatar ne, wanda suka rika tsakuro kadan-kadan ana aiwatarwa, a tsakanin wata 17, daga karshe kuma suka gabatar da dokoki sinfi- sinfi- har guda hudu, suka mika wa shugaban kasa shi kuma ya aika wa majalisa. Da aka yi karatun farko, sai shugaban kasa ya tafi Faransa tare da jamaarsa, yanzu kuma yana kasar Afirka da Kudu. A majalisar dattijai an yi karatun dokokin na biyu, wanda daga nan ne za a rabawa duk yan majalisar dattijai 109 kwafin wannan doka su koma su nazarceta. A wannan tsakanin ne ake sauraron masana, ake yin gyara, ake cirewa a saka sabo, ake muhawara a bainar jamaa.
Wannan shimfida ce
Bello Muhammad Sharada
At’tajdid News




