Jami’ar American Management University dake birnin London ta karrama Shugaban Hukumar Kula da Nagartar Ayyuka ta Kasa Dr. Baffa Babba Dan Agundi da sauran wasu mutane da Digirin girmamawa.
Da ya ke miƙa lambar Digirin girmamawar ga Dr. Baffa, Dr. Saf Buxy Wanda ya ce sun karrama Baffan ne bisa kokarinsa wajen gina rayuwar al’umma musamman a fannin ilimi da samawa matasa ayyukan yi.
Da yake jawabi Dr. Baffa Babba ya nuna farin cikinsa bisa wannan karramawar da aka yi musu.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu




