Sifaniya za ta karɓi tree ministocin ƙasashen Larabawa ranar Lahadi
A yau Lahadi Sifaniya za ta karɓi bakuncin ministocin ƙasashen Larabawa da Turai a wani taron samar da zaman lafiya a Gaza da mafitar kafuwar ƙasashe biyu masu cikakken iko a Gabas Ta Tsakiya.
Ƙasashen da za su halarci taron sun haɗa da Saudiyya da Masar da kuma Turkiyya.
Wakilin BBC ya ce gwamnatin Sifaniya, da ke yawan sukar Isra’ila, ta ce wannan taro an shirya shi ne da manufar kawo karshen zub da jini da yanayin jin-kai mai muni da ake ciki a Gaza.
Sannan taron na fatan ganin ya samar da hanyar tsagaita wuta da buɗe kofar kai isasshen agaji da kuma cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Hamas damar sakin ƴan Isra’ila da suka rage a hannunta.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




