By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: AN SAMI AMBALIYAR RUWA A JAHOHI 27 A NIGERIA.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > AN SAMI AMBALIYAR RUWA A JAHOHI 27 A NIGERIA.
News

AN SAMI AMBALIYAR RUWA A JAHOHI 27 A NIGERIA.

Attajdid
Last updated: 2024/08/17 at 1:01 PM
Attajdid Published August 17, 2024
Share
SHARE

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta bayyana cewa kawo yanzu ambaliyar ruwa ta shafi mutum 227,494 a jihohi 27 a faɗin ƙasar.A ƙiyasin da ta yi game da asarar da ambaliyar ruwan ta haifar, NEMA ta ce gidaje 32,837 da kadada 16,488 na gonaki da amfanin gona ne iftila’in ruwan ya lalata, a cewar wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Alhamis.NEMA ta yi gargaɗi ga mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a jihohin 27 da su soma ƙaura zuwa wasu wurare masu tsaro, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar

Mr. Manzo Ezekiel ya bayyana a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.”NEMA ta soma gudanar da aikin tantance yawan ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi tare da tura kayan agaji don tallafa wa al’umomin da iftila’in ya shafa,” in ji shi.Shugabar Hukumar, Zubaida Umar, ta jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa ga al’umomin yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa, tana mai ba da shawara da su koma wurare masu tudu yayin da ake cikin damina.

Kazalika shugabar ta yi kira kan a ƙara wayar da kawunan jama’a kan matakan da suka kamata su bi wajen kwashe shara don hana aukuwar ambaliyar ruwa a nan gaba.”Hukumar ta jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a game da hanyoyin sarrafa shara don hana ambaliyar ruwa tare da ba da shawara ga al’ummomin da ke cikin haɗarin fuskantar iftila’in da su koma wurare masu tudu da ba su da barazanar fuskantar ambaliyar,” in ji sanarwar.

NEMA ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin bayar da agajin gaggawa a matakin jihohi (SEMA) da shugabannin al’umomi, da su kasance cikin shiri a ko da yaushe don samar da tsare-tsare da shirin ko-ta-kwana kan ambaliya yayin da ake samun ƙaruwar iftila’in a wasu sassan Nijeriya.

nema.gov.ng.

At-tajdid News

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid August 17, 2024 August 17, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

An Soke Wasu Ma’aikatu An Hade Wasu a Tarayyar Nageriya 

Attajdid Attajdid October 25, 2024
Netanyahu da Gallant Suna Fuskantar Fishin Kotun ICC Kan Yakin Kare-Dangi da Suke Yi a Palestine.
Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba tallafi ga iyalan da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a garin Rinaye, karamar hukumar Shagari.
Germany withdraws troops from Niger Amidst Of Gaza Genocide
Ana Cigaba da Samun Rasa Rayuka da Munanan Raunuka a Harin da Iran Take Kaiwa Isra’ila 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?