A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar kano Comrd. Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
Ya ce Gwamnatin Kano ta amince da ware kudi naira miliyan dari da hamsin da daya da dubu dari takwas da sittin da uku da dari takwas da casa`in da biyar da kwabo casa`in da bakwai, domin aiwatar da wasu manyan ayyuka a garin.
Garin na Tiga Gadan dai shine wanda aka samu wani mutum ya hallaka mutane da yawa sakamakon sanya wuta a masallacin da ke garin yayin da Mutane suke gabatar da sallar Asuba
Ayyukan da gwamnatin Kano za ta aiwatar a garin sun hadar da sake Gina masallacin da Kuma ajujuwa biyu mai dauke da ofis.
Sai kuma gyaran bandakuna guda shida da Samar da Rijiyar Burtsatse mai amfani da hasken Rana wanda za ta kunshi babban tankin Ruwa.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS





