By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa gabanin babban taron MDD
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa gabanin babban taron MDD
International News

Birtaniya, Australia da Canada sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa gabanin babban taron MDD

Attajdid
Last updated: 2025/09/22 at 6:34 AM
Attajdid Published September 22, 2025
Share
SHARE

Ƙasashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka shiga cikin jerin ƙasashen Yamma da ke goyon bayan samun ‘yancin Falasɗinu yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba.

 

Wannan na zuwa ne a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza / Reuters

 

Ƙasashen Birtaniya, Canada, da Australiya a ranar Lahadi sun sanar da amincewarsu da Falasɗinu a matsayin ƙasa, inda suka shiga cikin jerin ƙasashen Yamma da ke goyon bayan samun ‘yancin Falasɗinu yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba.

 

Birtaniya

 

“A sakamakon wannan bala’in da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, muna ɗaukar mataki don tabbatar da yiwuwar zaman lafiya da mafitar two-state solution {wato ƙasashe biyu wadda kowace ke cin gashin kanta},” in ji Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a cikin wani bidiyo da ya fitar.

 

Ya ce wannan yana nufin samun Isra’ila mai aminci da tsaro tare da Falasdinu mai ɗorewa, inda ya ƙara da cewa: “A halin yanzu, ba mu da ko ɗaya.”

 

A watan Yuli, Firaministan ya ce Birtaniya za ta amince da Falasɗinu a watan Satumba idan gwamnatin Isra’ila ba ta ɗauki matakan da suka dace ba.

 

A gefe guda, gwamnatin Isra’ila ta bayyana matakin Birtaniya a matsayin “abin dariya” kafin sanarwar ta fito.

 

Kafin sanarwar, mataimakin Firaminista David Lammy ya shaida wa BBC cewa “yanzu lokaci ne da ya dace mu tsaya tsayin daka don mafitaf two-state solution.”

 

Canada

 

Firaministan Canada Mark Carney, a ranar Lahadi ya sanar da cewa ƙasarsa ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, tare da yin alƙawarin haɗin kai don gina zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila.

 

“Canada ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa kuma za ta bayar da haɗin kai wajen gina makoma mai zaman lafiya ga Falasɗinu da Isra’ila,” in ji Carney a shafin sada zumunta na X kafin taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

 

Sanarwar ta biyo bayan furucin Canada a baya na niyyar amincewa da Falasɗinu a lokacin zaman taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a watan Satumba 2025.

 

Australiya

 

Ita ma Australiya ta bi sahun takwarorinta wato Canada da Birtaniya wurin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa wanda wannan wani yunkuri ne na farfaɗo da mafita ta two-state solution wanda zai fara da tsagaita wuta a Gaza da sakin waɗanda aka kama a can, in ji Firaminista Anthony Albanese a cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa tare da Ministan Harkokin Waje Penny Wong.

 

A baya, Faransa, Luxembourg, da Malta sun sanar da shirin su na amincewa da Falasɗinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

 

Mai Rahoto

Mustapha Garba Usman

 

At’tajdid News

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 22, 2025 September 22, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra’ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da ƙasa biyu ba a yankin kasar Palastinu — Fidan

Attajdid Attajdid September 28, 2024
Ma’aikatan Jahar Zamfara sun yi barazanar Tafiya Yajin Aiki
Jigawa Hosts National Orphan”s Qur”anic Recitation Competition
SPEED ACTION TO END INSECURITY IN ZAMFARA, NORTH-WEST– PRESIDENT TINUBU CHARGES TROOPS
Russia takes Ukrainian Town in Advance on Pokrovsk
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?