Rundunar sojin Isra’ila ta ce an harba daruruwan makamai masu linzami cikin Isra’ila daga Iran.
A karon farko cikin shekaru da dama Iran ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango cikin birnin Tel-Aviv na Israila, wanda ke zama martani kan hare-hare da ƙasar ta Yahudawa ke kai wa Lebanon.




