MASU FAFUTUKA A KENYA SUN YI ZANGA-ZANGA AKAN GAZA
Mai rahoto: Zarumi Gusau
Masu fafutuka a Nairobi, babban birnin Kenya, sun fito kwansu da kwarkwata a kan babura domin yin Allah wadai da kisan kiyashi da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza.
A yayin zanga-zangar da aka gudanar ranar Lahadi, mahalarta sun rika rera taken: “A Ceci Falasdinawa, A Ceci Falasdinawa!”, domin nuna goyon baya da juriya ga al’ummar da ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
Rahotanni sun nuna cewa yawan Falasdinawan da Isra’ila ta kashe ya haura 62,000, abin da ya tayar da hankula a duniya baki ɗaya.
Wani daga cikin masu zanga-zangar ya bayyana cewa:
> “Dole ne a daina kisan kiyashi ga Falasdinawa. Yara suna mutuwa, mata na shan bakar wahala. Ana kai hare-hare a asibitoci da gidajen jama’a.”
Masu fafutukar sun yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakai na gaggawa wajen kawo ƙarshen jinin da ake zub da shi a Gaza.




