Kungiyar Jama´atut-Tajdidil Islamy (JTI) reshen Arewa maso gabashin Nigeria ta shirya mukhayyam (taron dalibai) wanda aka gabatar ranar Juma’a 20 ga wata zuwa Asabar 21 ga watan disamba
An gabatar da wannan taro a cibiyar yada Addinin musulunci ta Idris Alooma da ke Ajilari cross a cikin garin Maiduguri
An yi wa wannan taro take da
“NAGARTACCEN DALIBI TAFARKIN GINA AL´UMMA INGANTACCIYA´´
An Kuma gabatar da career guidance akan:
*Mass communication
*Nursing Science
*Pharmacy
Taron ya sami halartar jagororin dalibai na sassa daban daban da ga yankin Arewa maso gabas ciki harda General manager na Radio Hadin kai da kuma jagororin kungiyar dalibai musulmi (MSSN) na Jami´ar jihar Borno.
Abu Muhammad
At’tajdid News






