Al-Qassam Brigades sun kama wasu jirage marasa matuka na abokan gaba a gabashin birnin Rafah, kudu da zirin Gaza.
Hamas, tace kiran da aka samu daga asusun yahudawan sahyoniya da kuma kalaman shugabannin dakarun mamaya na mayar da yankin Falasdinu da na Larabawa wani shiri ne na fadada aikin yahudawan kama-wuri-zauna. ‘Yan mamaya na kira ga manyan gwamnatocin Larabawa domin tunkarar burinsu da kuma kokarin boye laifukansu.
Daya daga cikin fursunonin da aka sako Magdi Yasser Khalil daga sansanin Balata da ke Nablus ya hadu da mahaifiyarsa da kuma danginsa bayan ya shafe shekaru 21 a gidan yari.Fursunoni 54, ciki har da 35 daga Gaza, sun yi shahada tun farkon yakin Zirin Gaza kamar yadda Kungiyar Fursunonin Falasdinu ta bayyana.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan tayi Allah wadai da wallafar asusun Isra’ila na hukuma akan kafofin sada zumunta na taswirorin da ke ikirarin cewa na Isra’ila ne Taswirorin da ake zargin Isra’ila sun hada da wasu sassan yankunan Falasdinawa da ta mamaye, Jordan, Lebanon da Syria batun ya zo daidai da kalaman wariyar launin fata da Smotrich yayi kira da a hade yankin yammacin kogin Jordan da matsuguni a Gaza. Aljazeera Palestine.
Mai rahoto;
M.B.Gama.
At-tajdid News.






