Manchester City ta doke Manchester United a karawar da suka yi a cin kofin bude sabuwar kakar wasannin da ake kira ‘Community Shield’. Bayan tashi 1-1, City ta doke United da ci 7-6.
Wannan nasarar kamar ramako ne dangane da nasarar da United ta samu a kan City lokacin da ta lashe kofin FA. Wannan karawar itace ke bude sabuwar kakar firimiya ta Ingila a kowacce shekara. A makon gobe ne ake saran fara wasannin firimiyar na shekarar 2024/2025.
Manchester City ke rike da kofin sakamakon nasarar da ta samu na lashe kofin a kakar da ta gabata.
📷 Man City




