a LebanonA yayin da Isra’ila ke dab da kwashe watanni 12 tana luguden wuta a yankin Gaza na Falasɗinu, yanzu kuma ta mayar da hankali a kan ƙasar Lebanon, inda ta ƙaddamar da sabon yaƙi.Isra’ila ta matsa wurin kai hare-hare a Lebanon, inda ta kashe fiye da mutum 500 a cikin kwanaki kaɗan tare da mara dubbai da muhallansu bayan an kwashe watanni ana musayar wuta a kan iyakokin ƙasashen biyu.
Mahukunta a Tel Aviv sun yi iƙirarin cewa suna kai hari a yankunan da ƙungiyar Hezbollah take da ƙarfi, sai dai bayanai sun nuna cewa Isra’ila tana kai hari ne a kan fararen-hula kamar yadda majiyarmu ta yankin gabas ta tsakiya ta tsekuntamana.A yankin Gaza da aka mamaye, dakarun Isra’ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 41,000 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, tare da lalata galibin gine-ginen yankin.
At-tajdid News.




