Babban sufetan Yan sandar kasar nan Yace aikata miyagun laifuka na raguwa Sosae a Nigeria…..
Babban sifeton ƴan sanda na ƙasa ya ce aikata laifuffuka na raguwa sosai a Najeriya Sufeto Janar na ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya ce ana samun raguwar aikata laifuffuka a Najeriya duk da halin ƙuncin da wasu jama'a ke ciki. Egbetokun ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan wani taron sirri da suka yi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da Babban hafsan sojin ƙasa Laftanar Janar Christopher Musa. Sufeto Janar din ya ce alƙalumman da suke da shi na ƙararrakin da jama'a ke kai wa a ofishinsu, ya nuna cewar laifuffukan na raguwa. A na shi ɓangaren, Janar Musa ya ce za su mayar da hankali wajen murƙushe ɓarayin mai wadanda ke hana gwamnati samun kudaden da ya dace ta samu. Babban hafsan ya ce shugaban ƙasa na sane da halin da jama'a suke ciki, kuma yana ɗaukar matakan da suka dace.