By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Dakatar da Dokokin Haraji ta ƙasa a Majalisar Dattijan Nijeriya 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Dakatar da Dokokin Haraji ta ƙasa a Majalisar Dattijan Nijeriya 
News

An Dakatar da Dokokin Haraji ta ƙasa a Majalisar Dattijan Nijeriya 

Attajdid
Last updated: 2024/12/05 at 3:06 PM
Attajdid Published December 5, 2024
Share
SHARE

Majalisar Dattijan Nijeriya ta jingine batun ƙudurin dokokin haraji na Nijeriya da ake taƙaddama a kansu.

 

Mataimakain Shugaban majalisar Sanata Barau Jibrin ne ya sanar da haka, yayin da yake jagorantar zaman majalisar ta dattawa a ranar Laraba.

 

Sanata Barau ya ce an jingine batun ne saboda yadda ake ce-ce-ku-ce a kan ƙudurorin, da kuma tabbatar da cewa an yi duban tsananki kan ɓangarorin da wasu al’ummar ƙasar ke nuna damuwa a kai.

 

Ya ƙara da cewa an kafa wani kwamiti na majalisar dattijai ƙarƙashin Sanata Abba Moro da zai zauna da ofishin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’ar Ƙasar don duba ɓangarorin da suke janyo taƙaddama don a warware su.

 

“Mun yanke hukuncin jingine batun siyasa da ɓangaranci da ƙabilanci a gefe, mu zauna mu-ya-mu, don mu lalubo mafita kan batun Ƙudurorin Gyara kan Dokokin Haraji,” a cewar Sanata Barau.

 

“Mun sanar da ɓangaren zartarwa matsayarmu, kuma an amince cewa za a kafa wani kwamiti da zai zauna ya yi duba kan ɓangororin da ake taƙaddama a kansu don a warware su.”

 

Mataimakin shugaban na majalisar dattijai ya ce kwamitin, na da wakilai daga dukkan shiyyoyin ƙasar guda shida, da wasu kwamitoci da suka shafi kuɗi da banki da kasafin kuɗi na majalisar, da ma duka shugabannin majalisar, inda za su fara tattaunawa da Ministan Shari’a a ranar Alhamis.

 

Ya ce an ɗauki matakin ne “domin ƙasar ta Nijeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.”

 

“Za mu warware dukkan batutuwan kafin a bar komai ya wuce,” in ji Sanata Barau.

 

Sai dai Majalisar ta Dattijai ba ta bayyana lokacin da ɓangaranta da na ofishin Ministan Shari’ar ƙasar za su kammala tattaunawa kan batun ba.

 

Tun lokacin da shugaban Nijeriya ya aike da ƙudurori huɗu don yin gyare-gyare kan dokokin harajin ƙasar, ake ce-ce-ku-ce kan wasu ɓangarorin dokokin, bisa zargin cewa sauye-sauyen za su shafi yadda wasu jihohin ƙasar ke samun kuɗi daga rabon arzikin ƙasar da ake yi a duk wata.

 

Ɓangaren da ya fi jan hankali shi ne yadda za a sauya tsarin rabon harajin VAT, abin da wasu ke zargin cewa za a fifita wasu tsirarun jihohi a ƙara azurta su, yayin da za a ƙara talauta mafi yawan jihohin ƙasar.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid December 5, 2024 December 5, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ma’aikatan Jahar Zamfara sun yi barazanar Tafiya Yajin Aiki

Attajdid Attajdid November 20, 2024
Netanyahu Yana Tsoran Za a Kawo Masa Hari Daga Lebanon 
Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
Sojojin Nijeriya Shida da ‘Yan Boko Haram 34 Sun Mutu a Wata Arangama a Borno
Kamfanin NNPCL Ya Fitar Farashin Man Fetur na Matatar Dangote a Nigeria
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?