Wani sabon rahoto ya zargi gwamnatin Canada da yaudarar jama’arta dangane da ikirarin dakatar da fitar da makamai zuwa ƙasar Zionist, duk da cewa a 2023 ta sanar da daskarar da tallafin makamai.
RAHOTON MAI SHAFI 58 YA FAYYACE SIRRI
Rahoton wanda Palestinian Youth Movement, World Beyond War, da Arms Embargo Now suka haɗa, ya tabbatar da cewa:
An ci gaba da aika kayan yaƙi sama da 390 zuwa Isra’ila
Wasu daga cikin su an sake turasu ta Amurka, domin gujewa duba da fallasa
MAKAMAN DA AKA TURA
A cikin rahoton mai suna “Exposing Canadian Military Exports to Israel”, an bayyana cewa:
An aika alburusai fiye da 420,000
Sassan harsashi guda 735
Kayan aikin jirgin F-35 kamar na’urar radar, GPS da sauran kayan leƙen asiri
Dual-use items (kayan da za a iya amfani da su a farar hula da soja)
YAUDARA DON KWANTAR DA HANKALI
Rahoton ya nuna cewa sanarwar gwamnatin Prime Minister Justin Trudeau na dakatar da makamai, ba komai ba ne face dabara don rage fushin jama’a, yayinda a zahiri ake ci gaba da tallafa kisan kiyashi a Gaza.
SHARHIN BAYAN LABARAI
SHIN GWAMNATIN KANADA TANA RIGIMA NE DA GASKIYA KO TANA BADA MAKAMAN KISA A BOYE?
YA KAMATA AL’UMMAR DUNIYA SU FADAKAR DA JUNA KAN RAWAR DA MANYAN KASASHEN YAMMA KE TAKAWA WAJEN ZALUNCIN GAZA.
RAHOTO DAGA: Amb. Mujahid
AT-TAJDID NEWS




