By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Ya Yi Kakkausan Bayanai a  Gaban MDD Akan Irin Kisan Kare Dangi Da Isra’ila Take Yi a Gaza
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Ya Yi Kakkausan Bayanai a  Gaban MDD Akan Irin Kisan Kare Dangi Da Isra’ila Take Yi a Gaza
International News

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Ya Yi Kakkausan Bayanai a  Gaban MDD Akan Irin Kisan Kare Dangi Da Isra’ila Take Yi a Gaza

Attajdid
Last updated: 2024/09/25 at 3:07 AM
Attajdid Published September 25, 2024
Share
SHARE

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya matsa wa shugabannin kasashen duniya lamba da su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

“Ina gayyatar kasashen da har yanzu ba su amince da Falasdinu ba da su tsaya kan dama ta tarihi a wannan mawuyacin lokaci da kuma amincewa da kasar Falasdinu cikin gaggawa,” in ji Shugaba Erdogan a cikin jawabinsa ga Majalisar Dinkin Duniya a New York ranar Talata.Erdoğan ya kara da cewa, dole ne a daina jinkirin samar da kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta da kuma tabbatar da yankinta.

Shugaban na Turkiyya ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kasa daukar kwararan matakai na kawo karshen tashe-tashen hankula, yana mai jaddada cewa kungiyar ta yi kasa a gwiwa.”

A cikin ‘yan shekarun nan, Majalisar Dinkin Duniya ta kasa aiwatar da aikinta na tushe, sannu a hankali tana rikidewa zuwa tsarin da ba shi da inganci, mai wahala, da rashin aiki,” in ji Erdogan, yana mai jaddada bukatar yin kwaskwarima a cikin duniya.

Da ya karkata akalarsa kan halin da ake ciki a Gaza, Shugaba Erdogan ya yi Allah wadai da matakan da Isra’ila take dauka.

“Sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, Gaza ta zama makabartar yara da mata mafi girma a duniya,” in ji shi, yana mai jaddada munanan asarar rayukan fararen hula da ake samu.

Erdogan ya kuma yi kakkausar suka ga kafafen yada labarai na kasa da kasa, inda ya zarge su da rufe ido kan kisan da sojojin Isra’ila ke yi wa ‘yan jarida.”

Ga kungiyoyin watsa labarai na kasa da kasa, ina tambaya: Shin ba a kashe ‘yan jaridun a shirin talabijin da ake watsawa kai tsaye ba, kuma abokan aikinku Isra’ila ne suka kai farmaki ofishinsu?”

“Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi watsi da muhimman hakkokin bil adama, tana aiwatar da kisan kiyashi a fili ga wata al’umma tare da mamaye yankunansu mataki-mataki.

Falasdinawa suna amfani da halattaccen ‘yancinsu na tsayin daka kan wannan mamaya.””Me kuke jira don kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza?

“A wani kalubale kai tsaye ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Erdogan ya nuna shakku kan rashin daukar matakin da suka dace wajen fuskantar kisan kare dangi a Gaza.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, me kuke jira don dakatar da kisan kiyashin da ake yi a Gaza, ku ce ‘ya isa’ ga wannan zalunci, wannan dabbanci?

Erdogan ya kara da cewa, ba kananan yara kadai ba, har ma da tsarin Majalisar Dinkin Duniya na mutuwa a Gaza.. Gaskiyar dabi’un da Kasashen Yammacin Duniya ke ikirarin karewa suna mutuwa.

Ya kuma yi kakkausar suka ga wadanda ke da alhakin haddasa rashin zaman lafiya a yankin.

“Me kuke jira don dakatar da wannan hanyar tsari na kisan kiyashi da ke jawo duk yankin cikin yaƙi don burin siyasa?” Erdogan ya tambaya.

“Kamar yadda kawancen bil adama ya dakatar da Hitler shekaru 70 da suka gabata, dole ne a dakatar da Netanyahu da masu goya masa baya ta hanyar haɗin gwiwar bil adama.”

TRT Afarka Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid September 25, 2024 September 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

16 died, 3,936 Displaced By Flood In Jigawa.

Attajdid Attajdid August 14, 2024
GAME DA HUKUNCIN DONALD TRUMP AKAN NAJERIYA
Duk wanda bai zaɓi mahaifina ba zai gamu da fishina -Shugaban Sojin Uganda
Governor Namadi Appointed Ambassador For Maleria Eradication Campaign 
Israeli Minister Denounces UN Peacekeepers as Fighting Rages
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?