*GAME DA HUKUNCIN DONALD TRUMP AKAN NAJERIYA*
*SHIMFIDA*
A Karshe Dai Shugaban Amurka, Donald Trump, Ya Yanke Hukuncin Da Ya Yi Niyya Akan Najeriya Game Da Kaharun Da Wasu Daga Cikin Kiristocin Najeriya Suka Yi Na Cewar Ana Yi Musu Kisan Kiyashi A Najeriya. Daman Donald Trump Din Ya Taba Yankewa Najeriya Irin Wannan Hukuncin A Yayin Zangon Muliknsa Na Farko, Amman Da Joe Biden Ya Kada Shi A Zabe Sai Ya Soke Wannan ‘Danyan Hukuncin. Wannan Hukunci Kuwa Shine Na Cewar Amurka Za ta nemi Kasar Ta Dauki Wasu Matakai Na Kare Muradun Amurka, Idan Ba Haka Ba Za A Rika Kakabawa Kasar Takunkumi Kalakala. Alal Misali, Wadannan Muradu Za Su Iya Kasancewa Kamar Haka:
1. Duk Jahar Da Take Da Dokar Aiwatar Da Shari’ar Musulunci Ta Soke Wannan Dokar
2. Duk Jihar Da Take Da Dokar Hani Ga Batanci Ga Annabin Tsira (SAW) Lallai Ta Soke
3. Duk Wurin Da Kiristoci Suke Da Bukatar Gina Coci A Basu Dama Su Gina
4. Duk Abinda Kiristoci Suka Ce Hankalinsu Bai Kwanta Da Shi A Kasar Ba, Kamar Kasuwanci Nau’in Halal, To Kada A Yi Shi
5. Duk Kasuwancin Da Kiristoci Suke Da Bukata, Kamar Na Cinikin Giya, To A Barsu Su Yi A Fadin Kasar.
Wannan Kadan Kenan Na Misalai Da Suka Shafi Koken Da Wasu Kiristoci Suka Kaiwa Amurka. Za Ta Iya Yiwa Kuma A Shigar Da Wasu Bukatun Da Suka Shafi Gudanar Da Mulki Da Tafikantar Da Tattalin Arziki.
Wannan Hukuncin Da Shugaba Trump Ya Dauka Ya Yi Kama Da Abinda Amurka Ta Yiwa Kasar Iraqi A Zamanin Mulkin Saddam. Aka Zargi Iraqi Da Mallakar Makamin Kare Dangi Don Kawai A Farmata. Da Ace Adalci Ake Nema Da Sai A Auna Koken Wadanda Suka Kai Korafi Da Kariyar Da Hukumomin Najeriya Suka Bayar, Da Kuma Bayanan Da Kungiyoyin Musulmi Suka Bayar. Kai Hatta A Cikin Kiristocin Wasu Masu Hankali Da Adalci Sun Yi Bayani Sabanin Wanda Masu Korafin Suka Yi, Amman Duk A Banza. An Riga An Tsara Abinda Ake So A Yiwa Najeriya.
To Ko Me Ya Ragewa Hukumomi Da Yan Kasa Su Yi? Ga Nawa Tunanin:
*ABINDA YA KAMACI HUKUMOMIN NAJERIYA*
1. Hukumomi su cigaba da amfani da kofofin da suke a bude na diplomasiyya wajen ankarar da gwamnatin Trump cewar al’amarin nan fa ba haka yake ba. Ko Amurka ba ta yadda ba, sauran Duniyar masu hankali za su san duk wani mataki da Amurka ta dauka akan Najeriya, a dalilin wannan kaharun, zunzurutun zalunci ne. hakan kuwa akwai amfaninsa
2. Gwamnatin Najeriya ta fara rage dogaro da Amurka a fannoni da dama, kamar kasuwanci, da harkar ilimi, da kiwan lafiya, da sauransu. Ta mayar da hankali wajen karfafa alaka da wasu kasashen kamar Russia, da China, da Turkiyya
3. Gwamnati ta nemi hadin kan yan Najeriya, Musulmi da Kiristocin da ba su da wancan ra’ayi na kaharu, wajen juriya da tunkarar duk abinda ake son kullawa kasar na sharri.
*ABINDA YA KAMACI YAN KASA SU YI*
1. Duk ‘yan Najeriya, Musulmi da Kirista, su fara rage alakarsu da Amurka, musamman ta neman bizar zuwa Amurka, saboda ba lallai ta rika samuwa da sauki ba
2. Wadanda suke da kudi mai yawa a Dalar Amurka su canza su zuwa wani kudin na daban wadanda ake yin kasuwancin Duniya da su.
3. Duk Musulmi da yake da kyakkyawar alaka da wani Kirista kada ya bari wannan danbarwar ta shafi alakarsu; haka shima Kiristan da yake da alaka mai kyau da Musulmi, kada ya bari alakarsu ta baci
4. Kada Musulmi su raunana ko zuciyarsu ta karaya. Su lura cewar gata dai kam ba su da shi. Wanda ba Musulmi ba shi yake da gata. Yahudawa za su iya yiwa Musulmi kisan kiyashi, duk Duniya ta shaida, amman Amurka ta goyi bayan Yahudawa. A India ana yiwa Musulmi kisan kiyashi, amman babu ruwan Amurka. A China ana yiwa Musulmi kisan kiyashi, babu ruwan Amurka. A Najeriya babu gari daya tak da Musulmi suka kori Kirista suka mamaye garin amman Kirista sun kori Musulmi daga garin Tafawa Balewa sun mamaye garin. ‘Yan ta’addar da suke kisan kan mai-uwa-da-wabi a Najeriya sun fi kashe Musulmi akan Kirista, amman Trump ya fito karara ya ce shi rayukan Kirista kadai ne suka dame shi. To amman abinda zai kwantarwa da Musulmi hankali shine Musulunci dai yana ta yaduwa a Amurka da Turai. Wa ya sani ko idan ya gama mamayarsu ya zama daga Turai a Amurka Musulmi za su samu dauki, kuma Duniyar ma gaba daya ta samu gatan tsayar da adalci? Domin duk matsalar nan fa ta rashin adalci ce wacce tsarin Turai da Amurka suka dora Duniyar akai.
5. Su kansu al’umar Kiristocin Najeriya suna bukatar karin wayewa da cewar Yammacin Duniya fa ba damuwa suka yi da Kiristanci ba illa mallakar abinda yake hannun wadansu. Da gaske ne sun damu da rayukan Kiristoci da basu bari abinda yake faruwa a Kasar Kongo (kasar da tafi kowacce yawan Kirista a Duniya) ya na faruwa ba. Kiristoci a tsakaninsu suna ta kashe junansu. Haka ma abinda yake a South Sudan. Haka ma Central African Republic. Haka ya faru a Ruwanda. Ga misalai nan da yawa na Kasashen Kirista da ba a zaman lafiya. Kuma da zata baci Kiristocin Najeriya su nemi yin gudun hijira Kasar Amurka da za su gane cewa ba za ta karbe su ba. Don haka ya fi musu kyau su zauna lafiya da yan’uwansu a Najeriya.
6. A karshe, wajibin duk wadanda suka yi Imani ne su dage da addu’ar Allah ya tsare Najeriya daga dukkan wadanda suke nufinta da kowane irin sharri.
Wassalamu Alaikum wa Rahmatullah.
*_Dr. Saidu Ahmad Dukawa_*
BUK
1 – 11 – 2025




