By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Kasar Syria ta Shaki Iskar ‘Yanci Daga Kasar Amurka 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Kasar Syria ta Shaki Iskar ‘Yanci Daga Kasar Amurka 
News

Kasar Syria ta Shaki Iskar ‘Yanci Daga Kasar Amurka 

Attajdid
Last updated: 2025/05/14 at 5:12 PM
Attajdid Published May 14, 2025
Share
SHARE

Kasar Syria ta Shaki Iskar ‘Yanci Daga Kasar Amurka

 

 

 

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da Shugaban Amurka Donald Trump, da Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman da Shugaban Syria Ahmed Alsharaa sun yi wata ganawa ta yanar gizo, in ji kamfanin dillancin labarai na Anadolu a safiyar Laraba.

 

Shugaban Turkiyya ya ce matakin shugaban Amurka na janye takunkuman da aka saka wa Syria na da muhimmanci a tarihi.

 

A Riyadh, a ziyarar aiki ta farko da ya kai ƙasar wajen tun bayan dawo wa mulki a karo na biyu, ya zama shugaban kasar Amurka na farko da ya gana da shugaban kasar Syria.

 

Shugabannin biyu sun yi ganawa kafin babban taron shugabannin kasashen Yankin Tekun Fasha a Saudiyya a yayin ziyarar Trump a yankin, kamar yadda wani jami’in Fadar White House ya bayyana.

 

Babu wani shugaban Amurka da ya gana da shugaban Siriya tun bayan Bill Clinton da ya gana da Hafez Al Assad, mahaifin Bashar Al Assad a Geneva a shekarar 2000.

 

A ranar Talata Trump ya sanar da cewa zai janye “munanan” takunkuman da aka saka wa Siriya a zamanin Assad waɗanda ke karya tattalin arziki.

 

Matakin amsa ne ga kiran da ƙawayen Alsharaa Turkiyya da Saudiyya suka yi.

 

Isra’ila ta nuna rashin amincewar ta ga janye takunkuman, amma a ranar Talata Trump ya ce bin Salman da Erdogan ne suka ƙarfafa masa gwiwar janye takunkuman.

 

Trump ya ce ‘lokacin shanawar Syria’ ne yanzu kuma sauƙaƙa mata takunkuman zai ba su damar haɓaka.

 

‘Yan Siriya sun yi murnar samun wannan labarin, inda maza, mata da yara da yawa suka taru a dandalin Umayyad na Damascus.

 

Ma’aikatar Harkokin Wajen Siriya ta bayyana matakin na Trump da “Gaba mai muhimmanci” da zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali da lumana

 

 

Ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya

 

Rana ta farko ta ziyarar Trump a Gabas ta Tsakiya ta samu muhimman bukukuwa inda Saudiyya ta sha alwashin zuba jarin dala biliyan 600 a Amurka a kuma sayen makamai na dala biliyan 142 daga Amurkan.

 

Daga baya a ranar Laraba Trump ya wuce zuwa babban birnin Qatar Doha, domin ganawa da Sarki Tamim bin Hamd AlThani da sauran jami’an gwamnati.

 

Qatar, babbar ƙawar Amurka, ana sa ran za ta sanar da zuba jarin biliyoyin daloli a Amurka.

 

Bayan ziyartar Qatar, Trump zai wuce Abu Dhabi, inda zai gana da shugabannin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Alhamis.

 

Daga nan ne zai koma gida Washington a ranar Juma’a, amma ya ce akwai yiwuwar ya bi ta Turkiyya don halartar ganawar da Shugaban Rasha Vladimir Putin zai yi da Shugaban Ukraine Vladimri Zelensky a Istanbul.TRT Hausa.

 

Mai rahoto;

M.B.S.Gama.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid May 14, 2025 May 14, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Celebrating Icon @62:Governor Umar A. Namadi fca,

Attajdid Attajdid April 24, 2025
Turkiyya ce ta 11 a duniya wurin fitar da kayayyakin tsaro — Erdogan
Ana barazanar mika ɗan jarida Mustafa Ayash daga Hollanda zuwa Isra’ila — zanga-zangar neman sakin sa da kare ‘yancin jarida
MALAM AMINU ALIYU GUSAU TAFSIR 2 GA RAMADAN 1443/2022
JAMB TA DAUKI ALHAKIN FADUWAR JARRABAWA
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?