Ana Kokarin Cimma Yarjejiniyar Tsagaita Wuta a Gaza
Hamas ta ce ta cim ma yarjejeniya da jakadan Amurka Steve Witkoff kan tsarin tsagaita wuta na dindindin a Gaza kamar yadda TRT African Hausa ta kawo.
Ga karin bayani kan yarjejeniyar
– Ta hada da tsagaita wuta ta dindindin da cikakken ficewar Isra’ila daga Gaza.
– Shigar da kayan agajin jinƙai da nada kwamatin ƙwararru da zai kula da al’amuran yankin bayan sanarwar yarjejeniyar.
– Sakin fursunonin Isra’ila guda goma da wasu gawawwaki da dama a musanya da adadin. fursunonin Falasdinawan da aka amince da su, karkashin lamunin masu shiga tsakani.
– Hamas yanzu tana jiran amsa ta ƙarshe kan wannan tsarin.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




