At-tajdid News, ta sami sakon kugiyar Hamas daga majiyarta ta gabas ta tsakiya don bayyanawa duniya irin halin da Gaza da al’ummar ta suke ciki.
Hamas: –
“Muna kira ga al’ummarmu da kuma al’ummar duniya masu ‘yanci da su ci gaba da gwagwarmayar kauda zalunci da kisan kare dangi da amfani da yunwa a matsayin makamin yakar mutanan Gaza.”
“Ayi amfani da ranakun Juma’a da Asabar da Lahadi su kasance lokutan zanga-zangar nuna kyamar duniya kan ‘yan mamaya da magoya bayansu har sai an dakatar da wuce gona da iri.”
“Muna kira da a gudanar da ayyuka mafi fa’ida a cikin hadin gwiwa da shahidai Anas al-Sarif da Muhammad Qreikea da abokan aikinsu kan laifukan da ‘yan mamaya suka aikata kan ‘yan jarida.”
“Ga duniya baki daya, muna Allah wadai da cin zarafi na Sahayoniya da goyon bayan Amurka, kuma muna tir da kauda kai na shuwagabannin kasa da kasa.”
“Muna kira da a shiga cikin jerin gwano zanga-zanga a gaban ofisoshin jakadancin yahudawan sahyoniya da Amurka domin isarwa duniya sakon laifukan kisan kiyashi da yin amfani da yunwa a matsayin makamin yakar mutanan Gaza”
“Muna buƙatar a zaburar da masana da ɗalibai, domin su matsa lamba da ƙungiyoyinsu domin buɗe mashigar Gaza da ba da izinin shigar da magunguna, ruwa, da abinci.”
Mai rahoto.
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




